Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Rikicin Gabas ta Tsakiya ya yi ƙamari bayan Isra'ila ta kai hari a Iran

Iran ta ce an kai hare-hare da dama a babban birninta Tehran da birnin Karaj da ke maƙwabtaka yayin da mahukunta a Tel Aviv, da ke tsammanin ramuwar gayyar Iran suka ce sun "shiga cikin shiri sosai" domin kare kawunansu. Isra'ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a "wuraren aikin soji" na Ir...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:19
Rikicin Gabas ta Tsakiya ya yi ƙamari bayan Isra'ila ta kai hari a Iran
Kwa muhtasari

Iran ta ce an kai hare-hare da dama a babban birninta Tehran da birnin Karaj da ke maƙwabtaka yayin da mahukunta a Tel Aviv, da ke tsammanin ramuwar gayyar Iran suka ce sun "shiga cikin shiri sosai" domin kare kawunansu. Isra'ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a "wuraren aikin soji" na Ir...

Iran ta ce an kai hare-hare da dama a babban birninta Tehran da birnin Karaj da ke maƙwabtaka yayin da mahukunta a Tel Aviv, da ke tsammanin ramuwar gayyar Iran suka ce sun "shiga cikin shiri sosai" domin kare kawunansu. Isra'ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a "wuraren aikin soji" na Iran, kuma kafar watsa labaran Iran ta tabbatar da kai jin ƙarar fashewar abubuwa sannan ta ce wasu daga cikin ƙarararrakin an ji su ne daga na'urorin kakkaɓo makamai da ke Tehran babban birnin ƙasar. Babu babani game da ɓarnar da hare-haren waɗanda aka kai da sanyin safiyar Asabar suka yi a Iran sai dai kafofin watsa labaran ƙasar sun rawaito cewa an "ji manya ƙararraki" a Tehran da yankuna da ke gefensa sakamakon hare-hare ta sama. Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana "hare-haren a matsayin na yankan-shakku da aka kai kan wuraren sojojin Iran."