'Yan tawayen M23 sun yi iƙirarin ƙwace birnin Goma mai muhimmanci a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo. Ɗaruruwan ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo sun tsere zuwa maƙociyar ƙasar Rwanda, yayin da gomman sojojin sojojin Kongo ɗin suka “miƙa wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan tawayen M23 sun ƙwace iko da birnin Goma mai muhimmanci a Kongo. Wasu bidiyo da gidan Radio da Talabijin na Rwanda ya wallafa a shafin X, sun nuna wani abin da ke nuna kamar sojoji ne, wasu cikin kayan sarki, suna miƙa makamai ga jami’an tsaron Rwanda, bayan tsallakawa gabashin ƙasar mai maƙotaka ta kan babbar iyakar ƙasar a yankin Rubavu na Rwanda. Lamarin na baya-bayan nan ya zo ne sa’o’i bayan ‘yan tawayen M23 sun yi iƙirarin shiga Goma, abin da ya tilatsa wa mutane tsarewa daga birnin. ‘Yan tawayen na M23, waɗanda ake zargin suna samun goyon bayan Rwanda, sun zafafa hare-hare a gabashin Kongo a makon jiya, inda suka kwace muhimman birane. Sai dai Shugaban Rwanda Paul Kagame ya sha musanta zargin cewa yana goyon bayan ‘yan tawayen. Mummunan fasa gidan yari a Goma An fuskanci wani gagarumin fasa gidan yari da safiyar Litinin a birnin Goma na Kongo da aka yi wa kofar-rago, sa’o’i bayan mayaka daga ƙungiyar ‘yan tawaye ta M23 sun shiga birnin, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa AFP. An yi wa gidan yarin wanda yake da fursunoni kimanin 3,000 raga-raga, bayan ɓalla gidan yarin, abin da ya haifar da “mace-mace”, a cewar majiyoyin, ba tare da bayar da wani ƙarin bayani ba. Ana iya ganin fursounonin da suke tserewa a titunan da suka kusa da yankin, kamar yadda wani wakilin AFP ya bayyana.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Rikicin DRC: Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula sun tse zuwa Rwanda
'Yan tawayen M23 sun yi iƙirarin ƙwace birnin Goma mai muhimmanci a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo. Ɗaruruwan ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo sun tsere zuwa maƙociyar ƙasar Rwanda, yayin da gomman sojojin sojojin Kongo ɗin su...

A taƙaice
'Yan tawayen M23 sun yi iƙirarin ƙwace birnin Goma mai muhimmanci a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo. Ɗaruruwan ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo sun tsere zuwa maƙociyar ƙasar Rwanda, yayin da gomman sojojin sojojin Kongo ɗin su...
