Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Ribar da kamfanin mai na Saudi Aramco ke samu ta ragu

Saudi Aramco ya ce a shekarar 2022 ya samu ribar dala biliyan 161.07 amma a 2023 ya samu dala biliyan 121.25. Kamfanin mai na Saudi Aramco ya sanar da samun raguwa a ribar da ya samu a shekarar 2023 idan aka kwatanta da shekarun baya. A sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cew...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:19
Ribar da kamfanin mai na Saudi Aramco ke samu ta ragu
At a glance

Saudi Aramco ya ce a shekarar 2022 ya samu ribar dala biliyan 161.07 amma a 2023 ya samu dala biliyan 121.25. Kamfanin mai na Saudi Aramco ya sanar da samun raguwa a ribar da ya samu a shekarar 2023 idan aka kwatanta da shekarun baya. A sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cew...

Saudi Aramco ya ce a shekarar 2022 ya samu ribar dala biliyan 161.07 amma a 2023 ya samu dala biliyan 121.25. Kamfanin mai na Saudi Aramco ya sanar da samun raguwa a ribar da ya samu a shekarar 2023 idan aka kwatanta da shekarun baya. A sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa ya samu raguwa da kaso 24.7 cikin 100 a 2023 kuma hakan ya samo asali ne sakamakon faɗuwar farashin man fetur da kuma rage haƙo man. Saudi Aramco ya ce a shekarar 2022 ya samu ribar dala biliyan 161.07 amma a 2023 ya samu dala biliyan 121.25. “Wannan raguwar ta fito da tasirin raguwar farashin ɗanyen mai da kuma raguwa a adadin da ake sayarwa,” kamar yadda kamfanin ya sanar. Mamayewar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairun 2022 ya sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi, inda ya kai sama da dala 130 kan kowace ganga a shekarar. A rahoton da Aramco ya bayar ga gwamnatin ƙasar a 2022, ya ce riba ce ya samu mai tarihi sakamakon sai da ya bayar da rarar kuɗi a karon farko a kusan shekara goma. Hawa da saukar farashin mai Sai dai a bara, farashin mai ya ragu zuwa dala 85 a kowace ganga, wanda ya haifar da raguwa a ribar da ake samu. Ana sa ran farashin zai tashi zuwa kusan dala 88 a kowace ganga a bana, sakamakon rashin tabbas a duniya saboda yakin Isra'ila da Hamas, in ji wani kamfani mai zaman kansa na Riyadh Jadwa Investment a wani rahoto da aka buga a watan Oktoba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito. Zai iya kaiwa dala 90 kan kowacce ganga a karshen shekarar 2024, in ji Jadwa Investment. Ƙasar Saudiyya na daga cikin ƙasashen da suka fi haƙo ɗanyen man fetur a duniya