Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Real Madrid za ta kara da Atletico, Liverpool da PSG a zagayen 'yan 16 na gasar UEFA

A zagayen na sili-ɗaya-ƙwale na Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai, Bayern Munich za ta kara da abokiyar dabinta a Gasar Bundesliga wato Bayer Leverkusen sai ƙungiyar nan ta Faransa Paris Saint-Germain (PSG) za ta kara da ƙungiyar Liverpool ta Ingila. Ƙungiyar Real Madrid za ta kara da abokiyar hamayy...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:19
Real Madrid za ta kara da Atletico, Liverpool da PSG a zagayen 'yan 16 na gasar UEFA
En bref

A zagayen na sili-ɗaya-ƙwale na Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai, Bayern Munich za ta kara da abokiyar dabinta a Gasar Bundesliga wato Bayer Leverkusen sai ƙungiyar nan ta Faransa Paris Saint-Germain (PSG) za ta kara da ƙungiyar Liverpool ta Ingila. Ƙungiyar Real Madrid za ta kara da abokiyar hamayy...

A zagayen na sili-ɗaya-ƙwale na Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai, Bayern Munich za ta kara da abokiyar dabinta a Gasar Bundesliga wato Bayer Leverkusen sai ƙungiyar nan ta Faransa Paris Saint-Germain (PSG) za ta kara da ƙungiyar Liverpool ta Ingila. Ƙungiyar Real Madrid za ta kara da abokiyar hamayyarta Atletico Madrid a matakin sili-ɗaya-ƙwale a Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai ta UEFA. An tsara yadda zagayen na ‘yan 16 da zagayen dab da na kusa da na ƙarshe da zagayen dab da ƙarshe da kuma zagayen ƙarshe za su kasance a ranar Juma’a a Nyon. . A jadawalin da aka fitar, za a kammala gasar ta UEFA ta kakar 2024-2025 a ranar 31 ga Mayun 2025. Ga yadda jadawalin zai kasance: Zagayen ‘yan 16: 1- PSG da Liverpool 2- Club Brugge da Aston Villa 3- Real Madrid da Atletico Madrid 4- PSV Eindhoven da Arsenal 5- Feyenoord da Inter Milan 6- Bayern Munich da Bayer Leverkusen 7- Borussia Dortmund da Lille 8- Benfica da Barcelona