Marcus Rashford ɗan wasan Manchester United da ke zaman aro a Barcelona ya sha alwashin ci da ba da tallafin ƙwallo 30 zuwa 40 a kakarsa ta farko. Yayin da ya fara kakarsa ta farko a Barcelona cikin sa’a, Marcus Rashford ya sanya wa kansa gagarumin burin cin ƙwallaye a sabuwar ƙungiyarsa ta Barcelona. Rashford, wanda ke da kwantiragi da Manchester United, ya zo Barca ne a kakar bana a matsayin aro, inda ya fara samun sa’a ƙarƙashin koci Hansi Flick. A yanzu ɗan wasan mai shekaru 27 ɗan asalin Ingila yana so a ce zuwa ƙarshen kakar bana, ya ci ko ya ba da tallafin cin jimillar ƙwallo 30 zuwa 40. A halin yanzu bayan buga wa Barca wasanni 9 na La Liga da na Zakarun Turai, ya ci ƙwallo 2 kuma ya tallafa wajen cin ƙwallaye 4. A wasansu na farko na gasar Zakarun Turai a bana, Marcus Rashford ne ya ciyo wa Barcelona duka ƙwallaye biyun da ta ba su nasara kan Newcastle da ci 2-1.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Rashford ya sha alwashin kawo wa Barcelona kwallo 40 a bana
Marcus Rashford ɗan wasan Manchester United da ke zaman aro a Barcelona ya sha alwashin ci da ba da tallafin ƙwallo 30 zuwa 40 a kakarsa ta farko. Yayin da ya fara kakarsa ta farko a Barcelona cikin sa’a, Marcus Rashford ya sanya wa kansa gagarumin burin cin ƙwallaye a sabuwar ƙungiyarsa ta Barce...