Ana sa ran shugaban Rasha Vladimir Putin zai nada jakadan kasar a Burkina Faso bayan sake bude ofishin jakadancin rasha a kasar wanda aka rufe tun shekarar 1992. Kasar Rasha ta sake bude ofishin jakadancinta a Burkina Faso a ranar Alhamis bayan shafe kusan shekaru 32, a cewar sanarwar gwamnatin kasar da ke yankin Afirka ta Yamma da kuma jami’in diflomasiyyar Rasha suka fitar. An rufe ofishin ne a shekarar 1992, a cewar Jakadan Rasha a makwabciyar kasar Ivory Coast Alexei Saltykov, shugaban Rasha Vladimir Putin zai nada sabon jakadan Rasha a Burkina Faso. A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Burkina Faso ta fitar ta tabbatar da cewa "Rasha ta sake bude ofishin jakadancinta a yau Alhamis a Ouagadougou." Saltykov ya ce zai jagoranci ayyukan diflomasiyyar Rasha a Burkina Faso har sai an nada sabon jakadan, yana mai bayyana Burkina Faso a matsayin "tsohuwar abokiyar hulda da muke da kyakkyawar alaƙa ta abota." Sauya abokan hulda A bara Burkina Faso ta fuskanci juyin mulkin soji har sau biyu -- sun samo asali ne sakamakon rashin gamsuwa da kuma gazawar da aka yi wajen kawo karshen matsalar tsaro ta masu tada ƙayar baya. Tun bayan hawan su mulki a watan Satumban 2022, gwamnatin mulkin sojin kasar ta nesanta kanta daga Faransa, daɗaɗɗiyar abokiyar huldarta, sannan wacce ta mata mulkin mallaka, kana ta matsa kusa da Rasha. A watan Oktoba ne Burkina Faso ta kulla yarjejeniya da kasar Rasha kan gina tashar makamashin nukiliya domin kara samar da makamashi a yankin Sahel inda kasa da kashi daya cikin hudu na al'ummar kasar ke samun wutar lantarki.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Rasha ta sake bude ofishin jakadancinta a Burkina Faso bayan shekara 30
Ana sa ran shugaban Rasha Vladimir Putin zai nada jakadan kasar a Burkina Faso bayan sake bude ofishin jakadancin rasha a kasar wanda aka rufe tun shekarar 1992. Kasar Rasha ta sake bude ofishin jakadancinta a Burkina Faso a ranar Alhamis bayan shafe kusan shekaru 32, a cewar sanarwar gwamnatin k...

Bu haberde ne var?
Ana sa ran shugaban Rasha Vladimir Putin zai nada jakadan kasar a Burkina Faso bayan sake bude ofishin jakadancin rasha a kasar wanda aka rufe tun shekarar 1992. Kasar Rasha ta sake bude ofishin jakadancinta a Burkina Faso a ranar Alhamis bayan shafe kusan shekaru 32, a cewar sanarwar gwamnatin k...
