Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Ranar Farin Ciki ta Duniya: Ƙasashen Afirka da suka fi farin ciki

An nemi mutane a ƙasashe da yankuna 143 da su ƙimanta rayuwarsu daga matakin sifili zuwa 10, inda 10 ke nuna mafi kyawun rayuwarsu. Majalisar Ɗinkin Duniya ta saki wani jeri na ƙasashen da suka fi farin ciki a duniya, a yayin da ake bikin Ranar Farin Ciki ta Duniya ranar 20 ga watan Maris. Rahoto...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:19
Ranar Farin Ciki ta Duniya: Ƙasashen Afirka da suka fi farin ciki
De un vistazo

An nemi mutane a ƙasashe da yankuna 143 da su ƙimanta rayuwarsu daga matakin sifili zuwa 10, inda 10 ke nuna mafi kyawun rayuwarsu. Majalisar Ɗinkin Duniya ta saki wani jeri na ƙasashen da suka fi farin ciki a duniya, a yayin da ake bikin Ranar Farin Ciki ta Duniya ranar 20 ga watan Maris. Rahoto...

An nemi mutane a ƙasashe da yankuna 143 da su ƙimanta rayuwarsu daga matakin sifili zuwa 10, inda 10 ke nuna mafi kyawun rayuwarsu. Majalisar Ɗinkin Duniya ta saki wani jeri na ƙasashen da suka fi farin ciki a duniya, a yayin da ake bikin Ranar Farin Ciki ta Duniya ranar 20 ga watan Maris. Rahoton Ranar Farin Ciki ta Duniya na 2024 da aka wallafa a ranar Laraba ya nuna cewa Libiya ce ƙasar da ta fi farin ciki a Afirka. Daga ita sai ƙasar Mauritius da Afirka ta Kudu a nahiyar, inda Lesotho kuma ta zama ta ƙarshe a ƙasashen Afirka gaba ɗaya. A matakin duniya kuwa, Finland ce ta farko a jerin ƙasashen da suka fi farin ciki, sai Denmark da Iceland da Sweden, yayin da ƙasashe takwas na Afirka suka kasance daga cikin 10 na ƙarshe a jerin. Rayuwa mafi inganci An nemi mutane a ƙasashe da yankuna 143 da su ƙimanta rayuwarsu daga matakin sifili zuwa 10, inda 10 ke nuna mafi kyawun rayuwarsu. An yi amfani da sakamako na shekara uku da suka wuce don samar da jerin. A fayyace, gamsuwar rayuwa a yankin kudu da hamadar Sahara ya ƙaru a tsakanin matasa, ko da yake jin dadin matasa ya ragu a Arewacin Afirka. The annual World Happiness Report was launched in 2012 to support the United Nations' sustainable development goals. An kaddamar da rahoton jin dadin duniya na shekara-shekara a shekara ta 2012 don tallafawa manufofin ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya. Ƙasashe goman farko na Afirka da suka fi farin ciki a jerin na duniya Libya ce ta 66 a duniya Mauritius ce ta 70 a duniya Afirka ta Kudu ce ta 83 a duniya Algeria ce ta 85 a duniya Congo Brazzaville (Republic of Congo) ce ta 89 a duniya Mozambique ce ta 90 a duniya Gabon ce ta 95 a duniya Ivory Coast ce ta 96 a duniya Guinea ce ta 97 a duniya Senegal ce ta 99 a duniya Matsayin sauran ƙasashen Afirka a jerin duniya: 102 - Nijeriya 104 - Kamaru 107 - Maroko 109 - Nijar 110 - Burkina Faso 114 - Kenya 120 - Ghana 127 - Masar 130 - Habasha Kasashe goma mafi karancin farin ciki a Afirka a cikin jerin kasashen duniya: 131 - Tanzaniya 132 - Comoros 134 - Zambiya 135 - Eswatini 136 - Malawi 137 - Botswana 138 - Zimbabwe 139 - Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo 140 - Saliyo 141 - Lesotho A cikin binciken, an yi la'akari da ma'aunai na tallafin zamantakewa da samun kudin shiga da lafiya da 'yanci da karimci da rashin cin hanci da rashawa.