Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Pezeshkian da Jalili sun yi kankankan a yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri'u a zaɓen shugaban Iran

Sakamakon wucingadi na zaɓen shugaban Iran ya nuna cewa Saeed Jalili ne yake kan gaba yayin da Massoud Pezeshkian yake biya masa, lamarin da ke nuna cewa akwai yiwuwar a tafi zagaye na biyu ranar 5 ga watan Yuli idan ba a samu wanda ya yi nasara ba. Sakamakon da aka fitar kawo yanzu na zaɓen shug...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:19
Pezeshkian da Jalili sun yi kankankan a yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri'u a zaɓen shugaban Iran
A taƙaice

Sakamakon wucingadi na zaɓen shugaban Iran ya nuna cewa Saeed Jalili ne yake kan gaba yayin da Massoud Pezeshkian yake biya masa, lamarin da ke nuna cewa akwai yiwuwar a tafi zagaye na biyu ranar 5 ga watan Yuli idan ba a samu wanda ya yi nasara ba. Sakamakon da aka fitar kawo yanzu na zaɓen shug...

Sakamakon wucingadi na zaɓen shugaban Iran ya nuna cewa Saeed Jalili ne yake kan gaba yayin da Massoud Pezeshkian yake biya masa, lamarin da ke nuna cewa akwai yiwuwar a tafi zagaye na biyu ranar 5 ga watan Yuli idan ba a samu wanda ya yi nasara ba. Sakamakon da aka fitar kawo yanzu na zaɓen shugaban ƙasar Iran ya nuna cewa tazarar ƙuri'u 200,000 ne tsakanin Saeed Jalili, wanda ya samu kashi 42, da Masoud Pezeshkian, wanda ya samu kashi 41. A yayin da aka ƙidaya sama da ƙuri'u miliyan 8 a ranar Asabar, an soma hasashen tafiya zagaye na biyu idan ba a samu wanda ya yi nasara kai-tsaye a zagayen farko ba. Alƙaluman farko da aka fitar waɗanda ba a hukumance ba, sun nuna ɗan takarar da ke neman kawo sauyi Pezeshkian, yana kan gaba inda yake da kashi 42.6, yayin da Jalili yake biye da shi da kashi 38.8. Wannan sakamakon ya nuna yadda 'yan takarar biyu suka yi kankankan, abin ake hasashen zai tilasta a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen ranar 5 ga watan Yuli. Al'ummar Iran suna zaɓen shugaban ƙasa yayin da ake tsaka da tunzuri a yankin An soma fitar da sakamakon zaɓen ne bayan an shafe awanni 18 ana kaɗa ƙuri'a. Kakakin hedkwatar hukumar zaɓen ƙasar Iran, Mohsen Eslami, ya ce an kammala jefa ƙuri'a ne da tsakar dare a agogon ƙasar. An soma kaɗa ƙuri'a ne ranar Juma'a da misalin ƙarfe 8 na safe sannan aka ce za a kammala zaɓe da ƙarfe 6 na yamma, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada. Sauyi a harkokin siyasar Iran Sai dai sau uku Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar, wadda take da alhakin gudanar da zaɓen, ta tsawaita lokacin jefa ƙuri'a. 'Yan takara huɗu ne suke neman shugaban ƙasar — Mohammad Baqer Qalibaf, Jalili, Pezeshkian da Mostafa Pourmohammadi — bayan rasuwar Ebrahim Raisi sakamakon hatsarin jirgin helikwafta a watan jiya. An ƙiyasta cewa mutum kimanin miliyan 64 suka cancanci kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban Iran, galibinsu kuma matasa ne. A zaɓen shugaban ƙasa na 2021, mutum miliyan 59.3 suka cancanci kaɗa ƙuri'a. An ajiye akwatunan zaɓe kimanin 58,640 a faɗin ƙasar domin sauƙaƙa wa mutane kaɗa ƙuri'a, kuma akwatu 6,000 daga cikinsu an ajiye su ne a Tehran.