Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Osimhen ya isa Turkiyya, ya shirya taka leda a ƙungiyar Galatasaray

Bidiyon da aka fitar a shafukan sada zumunta ya nuna Osimhen na ɗaga hannaye ga magoya baya da ke kaɗa tutar Galatasaray a yayin tarbarsa a filin jiragen sama a ranar Litinin. Ɗan wasan gaba na Nijeriya Victor Osimhen ya isa Istanbul, Turkiyya, don kammala tattaunawar dawowarsa ƙungiyar ƙwallon ƙ...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:19
Osimhen ya isa Turkiyya, ya shirya taka leda a ƙungiyar Galatasaray
Kwa muhtasari

Bidiyon da aka fitar a shafukan sada zumunta ya nuna Osimhen na ɗaga hannaye ga magoya baya da ke kaɗa tutar Galatasaray a yayin tarbarsa a filin jiragen sama a ranar Litinin. Ɗan wasan gaba na Nijeriya Victor Osimhen ya isa Istanbul, Turkiyya, don kammala tattaunawar dawowarsa ƙungiyar ƙwallon ƙ...

Bidiyon da aka fitar a shafukan sada zumunta ya nuna Osimhen na ɗaga hannaye ga magoya baya da ke kaɗa tutar Galatasaray a yayin tarbarsa a filin jiragen sama a ranar Litinin. Ɗan wasan gaba na Nijeriya Victor Osimhen ya isa Istanbul, Turkiyya, don kammala tattaunawar dawowarsa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray SK daga Napoli. Galatasaray ta ƙudiri niyyar ƙara Osimhen a tawagar 'yan wasanta bayan kammala Gasar Premier ta Ingila da Rufe Sayen 'Yan wasa a Saudiyya inda aka gaza sayen ɗan wasan gaban mai shekara 25. Bidiyon da aka fitar a shafukan sada zumunta ya nuna Osimhen na daga hannaye ga magoya baya da ke kaɗa tutar Galatasaray a yayin tarbarsa a filin jiragen sama ranar Litinin da daddare. "Victor Osimhen ya iso Istanbul," in ji wani saƙo da Galatasaray ta fitar ta shafin X. "Yanayin na da matuƙar kyau. Magoya baya mafi nagarta a duniya na nan wajen. Na ji daɗin kasancewa ta a nan. Ina farin ciki sosai. Na zaƙu na ga magoya baya a filin wasa. Zan yi musu iya ƙoƙarina," in ji Osimhen a gajeren bayanin da ya yi a filin jirgin saman. Ɗan wasan gaban ya bar filin jirgin a wata mota ta musamman tare da Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Galatasaray Ibrahim Hatipoglu da Daraktan Ƙwallon Ƙafa Cenk Ergun.