Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Obasanjo ya musanta neman wa’adi na uku, ya ce da ya ga dama da ya samu

“Ni ba wawa ba ne. Da a ce ina son wa’adi na uku, na san yadda zan yi na nema. Kuma babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai ce na kira shi na gaya masa ina son wa’adi na uku,” in ji tsohon shugaban ƙasar. Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya karyata zargin da aka jima ana yi m...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:18
Obasanjo ya musanta neman wa’adi na uku, ya ce da ya ga dama da ya samu
Em resumo

“Ni ba wawa ba ne. Da a ce ina son wa’adi na uku, na san yadda zan yi na nema. Kuma babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai ce na kira shi na gaya masa ina son wa’adi na uku,” in ji tsohon shugaban ƙasar. Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya karyata zargin da aka jima ana yi m...

“Ni ba wawa ba ne. Da a ce ina son wa’adi na uku, na san yadda zan yi na nema. Kuma babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai ce na kira shi na gaya masa ina son wa’adi na uku,” in ji tsohon shugaban ƙasar. Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya karyata zargin da aka jima ana yi masa kan cewa ya taɓa neman tsawaita wa’adin mulkinsa, inda ya jaddada cewa bai taɓa neman wa’adi na uku ba. Ya bayyana haka ne a yayin wani taro na Democracy Dialogue da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a Accra, Ghana. Obasanjon ya ce babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai iya cewa gaskata cewa ya taɓa roƙon goyon baya domin neman wa’adi na uku. “Ni ba wawa ba ne. Da a ce ina son wa’adi na uku, na san yadda zan yi na nema. Kuma babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai ce na kira shi na gaya masa ina son wa’adi na uku,” in ji tsohon shugaban ƙasar. Obasanjo ya jaddada cewa a zamanin mulkinsa ya nuna ƙwarewarsa wajen cim ma manufofin ƙasa da ke da wuyar cimmawa, inda ya kawo misalin yadda Nijeriya ta samu afuwar bashi a lokacin mulkinsa a matsayin babban ƙalubale fiye da neman wa’adi na uku.