الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

NUPENG ta fasa yin yajin aiki bayan ta ƙulla yarjejeniya da matatar mai ta Dangote

An cim ma yarjejeniyar ce a wata tattaunawa ta sirri da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kira kuma Ministan Kuɗi da wakilan ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya (NLC) suka halarta. Ƙungiyar ƙwadago ta direbobin tirelolin dakon mai a Nijeriya (NUPENG) ta yi shelar dakatar da shirinta na soma yajin aikin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:18 ص
NUPENG ta fasa yin yajin aiki bayan ta ƙulla yarjejeniya da matatar mai ta Dangote
لمحة سريعة

An cim ma yarjejeniyar ce a wata tattaunawa ta sirri da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kira kuma Ministan Kuɗi da wakilan ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya (NLC) suka halarta. Ƙungiyar ƙwadago ta direbobin tirelolin dakon mai a Nijeriya (NUPENG) ta yi shelar dakatar da shirinta na soma yajin aikin...

An cim ma yarjejeniyar ce a wata tattaunawa ta sirri da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kira kuma Ministan Kuɗi da wakilan ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya (NLC) suka halarta. Ƙungiyar ƙwadago ta direbobin tirelolin dakon mai a Nijeriya (NUPENG) ta yi shelar dakatar da shirinta na soma yajin aikin bayan ta ƙulla yarjejeniya da shugabannin matatar mai ta Dangote kan amincewa da ‘yancin ma’aikata na shiga ƙungiyoyin ƙwadago. An cim ma yarjejeniyar ce a wata tattaunawar sirri da hukumar tsaro ta farin kaya ta ƙasar (DSS) ta jagoranta kuma Ministan Kuɗi da wakilan ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya suka halarta. Muƙaddashin sakataren NLC, Benson Upah, ne ya tabbatar da sakamakon tattaunawar yayin da ma’aikatar ƙwadagon Nijeriya ta ce za ta fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba. An cim ma wannan matsaya ne a tattunawar da ma’aikatar ƙwadagon tarayya ta jagoranta ranar Litinin 8 ga watan Satumba bayan NUPENG tayi barazanar soma yajin aiki kan yadda kamfanin ya ƙi amincewa da ‘yancin ma’aikatansa na shiga ƙungiyar ƙwadago. Fahimtar Juna