Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

NNPCL zai fara lodin man fetur daga matatar Dangote ranar 15 ga Satumba

Jama’a da dama a faɗin Nijeriya na fata za a samu sauƙin farashi idan matatar ta Dangote ta soma samar da man fetur a ƙasar. Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa a ranar Lahadi 15 ga Satumba za a soma lodin kashi na farko na man fetur daga matatar mai ta Dangote da ke Legas. Kwamitin shugaban N...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:18
NNPCL zai fara lodin man fetur daga matatar Dangote ranar 15 ga Satumba
Kwa muhtasari

Jama’a da dama a faɗin Nijeriya na fata za a samu sauƙin farashi idan matatar ta Dangote ta soma samar da man fetur a ƙasar. Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa a ranar Lahadi 15 ga Satumba za a soma lodin kashi na farko na man fetur daga matatar mai ta Dangote da ke Legas. Kwamitin shugaban N...

Jama’a da dama a faɗin Nijeriya na fata za a samu sauƙin farashi idan matatar ta Dangote ta soma samar da man fetur a ƙasar. Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa a ranar Lahadi 15 ga Satumba za a soma lodin kashi na farko na man fetur daga matatar mai ta Dangote da ke Legas. Kwamitin shugaban Nijeriya kan sayar da ɗanyen mai ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a a Abuja. Shugaban hukumar tattara haraji ta Nijeriya Zach Adedeji wanda mamba ne a kwamitin ya bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Oktoba, kamfanin na NNPCL zai soma bayar da ganga 385 ta ɗanyen mai a kullum ga matatar Dangote. Ya ƙara da cewa ita kuma matatar ta Dangote za ta bayar da fetur da man dizel wanda ya zo daidai da darajar man a kasuwa kuma a biya kuɗin a naira. An shafe lokaci ana kwan-gaba kwan-baya tsakanin kamfanin na NNPCL da kuma matatar ta Dangote dangane da batun ciniki da hada-hada ta ɗanyen mai. Haka kuma duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu ƙarin kuɗin mai a Nijeriya, lamarin da ya ƙara saka ‘yan ƙasar da dama ƙorafi. A farkon watan nan ne aka wayi gari gidajen mai mallakar kamfanin na NNPCL sun ƙara farashin da ake sayar da man fetur ɗin. Sai dai jama’a da dama a faɗin ƙasar na fata za a samu sauƙin farashi idan matatar ta Dangote ta soma samar da man fetur a ƙasar.