Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Nijeriya za ta koyi ingantar wutar lantarki daga Masar – Minista

Adelabu ya bayyana ƙoƙarin Nijeriya, nasa da mutanen karkara da ke nesa da lantarki ta hanyar tsare-tsaren samar da makamashi da za a iya sabuntawa, yana mai bayyana matsalolin da ke tattare da ƙoƙarin faɗaɗa wutar lantarkin ƙasar zuwa kowane yanki. Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce za ta koyi ya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:18
Nijeriya za ta koyi ingantar wutar lantarki daga Masar – Minista
Em resumo

Adelabu ya bayyana ƙoƙarin Nijeriya, nasa da mutanen karkara da ke nesa da lantarki ta hanyar tsare-tsaren samar da makamashi da za a iya sabuntawa, yana mai bayyana matsalolin da ke tattare da ƙoƙarin faɗaɗa wutar lantarkin ƙasar zuwa kowane yanki. Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce za ta koyi ya...

Adelabu ya bayyana ƙoƙarin Nijeriya, nasa da mutanen karkara da ke nesa da lantarki ta hanyar tsare-tsaren samar da makamashi da za a iya sabuntawa, yana mai bayyana matsalolin da ke tattare da ƙoƙarin faɗaɗa wutar lantarkin ƙasar zuwa kowane yanki. Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce za ta koyi yadda ake samo tare da yaɗa wutar lantarki daga Masar wadda ta bayyana a matsayin abin koyi a fannin. Gwamnatin ta kuma tabbatar da jajircewarta kan raya karkara ta hanyar inganta samar da wutar lantarki. Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana wannan ne a lokacin wata ganawa a Abuja da jakadan Masar a Nijeriya, Mohammed Fouad. Wata sanarwa da mai magana da yawun Adelabu, Bolaji Tunji, ya fitar ranar Lahadi ta ce ganawar ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu wajen faɗaɗa samar da makamashi, tare da mayar da hankali kan makamashin da ake sabuntawa da samar da lantarki a karkara. Adelabu ya yaba da nasarorin da Masar ta samu a fannin makamashi, yana mai bayyana ƙasar a matsayin abar koyi wajen inganta makamashi. Ya bayyana sha’awar Nijeriya na ta yi koyi da Masar wajen samarwa da yaɗawa da kuma raba wutar lantarki, yana mai ƙarawa da cewa nasarar da Masar ta samu ne ya sa Nijeriya ta fara aiki da kamfanin Siemens domin daidaita fannin wutar lantarkin Nijeriya. “Masar ta samu gagarumin ci-gaba wajen haɓaka fannin makamashinta, kuma muna shauƙin haɗin gwiwa da koyo daga ƙwarewarku. Munafarmu ita ce tabbatar da samun makamashi mai ɗorewa mai araha ga dukkan ‘yan Nijeriya,” in ji shi. Adelabu ya bayyana ƙoƙarin Nijeriya na sa da mutanen karkara da ke nesa da lantarki ta hanyar tsare-tsaren samar da makamashi da za a iya sabuntawa, yana mai bayyan matsalolin da ke tattare da ƙoƙarin faɗaɗa wutar lantarkin ƙasar zuwa ko wane yanki. “Ba za a iya sada yankunan karkara da yawa da wutar lantarkin ƙasa ba saboda matsaloli na tattalin arziƙi, amma ba za mu iya watsi da su ba. Ta hanyar shirinmu na samar da makamashi da za a iya sabuntawa, muna cike giɓin da ke akwai. “Mun samu kuɗi da yawa ciki har da dala miliyan $750 daga shirin DARES na Bankin Duniya da kuma ƙarin dala miliyan 190 daga hukumar ba da agaji ta Japan domin taimaka wa wannan shirin,” in ji Adelabu. Ya jaddada cewa albarkatun makamashin da ake iya sabuntawa na Nijeriya ciki har da hasken rana da iska da kuma makamashin da za a iya samu ta ƙarfin gudun ruwa, yana mai bayyana jajircewar ƙasar wajen amfani da waɗannan albarkatun domin samun lantarki mai ɗorewa. A nasa jawabin, Fouad ya bayyana sha’awar Masar ta aiki da Nijeriya, musamman wajen cike giɓin samar da mita da kuma koyar da yadda ya dace a gudanar da aikin samar da lantarki. Ya jaddada manufofi da kuma fa’idojin da ƙasashen biyu suke son su cim ma wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu. “Nijeriya da Masar suna da abubuwa da yawa da suka haɗa su da kuma yiwuwar haɗa kai a fannin makamashi. Za mu yi aiki tare domin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin makamashin ƙasashen biyu,” in ji Fouad.