Ƙaddamar da alluran riga-kafin na ranar Alhamis ya samu halartar jami'ai daga Ma'aikatar Lafiya da Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Nijeriya (NPHCDA) da kuma sauran abokan hulɗa. Nijeriya ta karbi kason farko na allurar riga-kafin cutar maleriya R21 har 846,000 daga kamfanin Gavi, the Vaccine Alliance. Ƙaddamar da alluran riga-kafin na ranar Alhamis ya samu halartar jami'ai daga Ma'aikatar Lafiya da Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Nijeriya (NPHCDA) da kuma sauran abokan hulɗa. Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate, ya bayyana isowar alluran riga-kafin a matsayin wata muhimmiyar nasara a ƙoƙarin gwamnati na kawar da cutar maleriya daga ƙasar. Ya ce za a fara rarraba alluran ne a jihohin da suka fi fama da cutar, musamman Kebbi da Bayelsa,, kuma za a yi amfani da su a matsayin maganin warkar da cutar. Minista Pate ya kuma warware zare da abawa a kan ingancin riga-kafin, yana mai ba da tabbacin cewa yana da matuƙar tasiri ga warkar da cutar maleriya. Kazalika, Darakta Janar na hukumar NPHCDA, Muyi Aina ya yi bayani kan yadda za a rarraba su, yana mai cewa za a kafa tawagar da za ta tabbatar cewa an tsara yadda komai zai kasance tun daga rarrabawa har zuwa yi wa mutane a kan lokaci. Aina ya ce ana sa ran za a sake karbar wasu alluran 140,000 a 'yan watanni masu zuwa. Za a dinga yin wannan allura ne sau biyu ga duk mutum daya.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Nijeriya ta karɓi alluran riga-kafin maleriya 846,000
Ƙaddamar da alluran riga-kafin na ranar Alhamis ya samu halartar jami'ai daga Ma'aikatar Lafiya da Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Nijeriya (NPHCDA) da kuma sauran abokan hulɗa. Nijeriya ta karbi kason farko na allurar riga-kafin cutar maleriya R21 har 846,000 daga kamfanin Gavi,...

Ƙaddamar da alluran riga-kafin na ranar Alhamis ya samu halartar jami'ai daga Ma'aikatar Lafiya da Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Nijeriya (NPHCDA) da kuma sauran abokan hulɗa. Nijeriya ta karbi kason farko na allurar riga-kafin cutar maleriya R21 har 846,000 daga kamfanin Gavi,...
