Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Nijeriya ta kaddamar da shafin intanet na albarkatun ma'adinai ga masu zuba jari

Ana iya ziyartar shafin intanet din, mai suna 'Nigeria Mineral Resources Decision Support System' (NMDSS) kana yana ƙunshe da bayanai game da ilimin ƙasa da albarkatun ma'adinan Nijeriya. A wani yunkuri na kara samun saukin yin kasuwanci a bangaren ma’adinai, gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da wan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:18
Nijeriya ta kaddamar da shafin intanet na albarkatun ma'adinai ga masu zuba jari
Kwa muhtasari

Ana iya ziyartar shafin intanet din, mai suna 'Nigeria Mineral Resources Decision Support System' (NMDSS) kana yana ƙunshe da bayanai game da ilimin ƙasa da albarkatun ma'adinan Nijeriya. A wani yunkuri na kara samun saukin yin kasuwanci a bangaren ma’adinai, gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da wan...

Ana iya ziyartar shafin intanet din, mai suna 'Nigeria Mineral Resources Decision Support System' (NMDSS) kana yana ƙunshe da bayanai game da ilimin ƙasa da albarkatun ma'adinan Nijeriya. A wani yunkuri na kara samun saukin yin kasuwanci a bangaren ma’adinai, gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da wani shafin intanet ga masu son zuba jari a fannin ma'adinai a ranar Talata. Ana sa ran shafin zai na samar da cikakkun bayanai game da albarkatun ma'adinai, da kuma kayan aiki da ababben more rayuwa, a cewar sanarwar da ma'aikatar ma'adinai ta kasar ta fitar. “A baya, idan kana son saka hannun jari daga kasashen waje, dole sai ka zo Nijeriya don samun cikakkun bayanan da ake buƙata, amma da zuwa shafin nan, duk inda kake a duniya, da hannu daya kawai za ka iya samun duk wasu bayanai da kake bukata kama daga sanarwar da kuma shawarwari kan zuba jari," a cewar Dele Alake, Ministan Ma'aikatar Ma'adinai ta Nijeriya. Kasar da ke kan gaba wajen hako danyen mai a nahiyar Afirka, kana wadda ke da arzikin ma'adinan zinari da farauta da zinc, tana son masana'antar hakar ma'adinai ta taka rawar gani sosai a kokarinta na karkatar da tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur. Ana iya ziyartar shafin intanet din, mai suna 'Nigeria Mineral Resources Decision Support System' (NMDSS) kana yana ƙunshe da bayanai game da ilimin ƙasa da albarkatun ma'adinan Nijeriya. Nijeriya dai na kokarin janyo hankalin masu zuba jari a fannin hakar ma'adinai wanda ya dade babu wani ci gaban a zo a gani. Fannin na samarwa Nijeriya kasa da kashi 1 cikin 100 na yawan albarkatun tattalin arzikin da kasar ke samu.