Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Nijeriya ta amince da karbo bashin dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka

Nijeriya na ciyo bashi daga hukumomin kudi na kasa da kasa irin su Bankin Duniya, Asusun Bayar da Lamuni na Duniya da Bankin Raya Kasashen Afirka. Majalisar Zartarwar Nijeriya ta amince da karbo lamunin gata na dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka AfDB, a cewar Ministan Kuɗi Olawale...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:18
Nijeriya ta amince da karbo bashin dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka
Kwa muhtasari

Nijeriya na ciyo bashi daga hukumomin kudi na kasa da kasa irin su Bankin Duniya, Asusun Bayar da Lamuni na Duniya da Bankin Raya Kasashen Afirka. Majalisar Zartarwar Nijeriya ta amince da karbo lamunin gata na dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka AfDB, a cewar Ministan Kuɗi Olawale...

Nijeriya na ciyo bashi daga hukumomin kudi na kasa da kasa irin su Bankin Duniya, Asusun Bayar da Lamuni na Duniya da Bankin Raya Kasashen Afirka. Majalisar Zartarwar Nijeriya ta amince da karbo lamunin gata na dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka AfDB, a cewar Ministan Kuɗi Olawale Edun a ranar Litinin. Edun ya shaida wa manema labarai bayan wani taron majalisar ministocin da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar cewa, akwai kudin ruwa kashi 2.4 kan bashin wanda aka bayar na tsawon shekara 25, amma za a daga kafa na shekara takwas idan lamunin ya wuce ba a biya ba. “(Majalisar zartarwa ta tarayya) ta amince da wani rancen rangwame na dala biliyan daya don tallafa wa kasafin kudin kasar gaba daya da kuma amfani da shi wajen inganta samar da kudaden waje a kasar," in ji Edun, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.