Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Tinubu ya ƙaddamar da Tsarin Tattalin Arzikin Halal na Ƙasa

Nijeriya na shirin cin gajiyar kasuwar halal ta duniya mai darajar dala tiriliyan 7.7 Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da Tsarin Tattalin Arzikin Halal na Ƙasa domin bai wa ƙasar damar cin gajiyar kasuwar halal ta duniya wadda aka ƙiyasta darajarta ta kai dala tiriliyan 7.7, tare da faɗa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:18
Tinubu ya ƙaddamar da Tsarin Tattalin Arzikin Halal na Ƙasa
Kwa muhtasari

Nijeriya na shirin cin gajiyar kasuwar halal ta duniya mai darajar dala tiriliyan 7.7 Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da Tsarin Tattalin Arzikin Halal na Ƙasa domin bai wa ƙasar damar cin gajiyar kasuwar halal ta duniya wadda aka ƙiyasta darajarta ta kai dala tiriliyan 7.7, tare da faɗa...

Nijeriya na shirin cin gajiyar kasuwar halal ta duniya mai darajar dala tiriliyan 7.7 Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da Tsarin Tattalin Arzikin Halal na Ƙasa domin bai wa ƙasar damar cin gajiyar kasuwar halal ta duniya wadda aka ƙiyasta darajarta ta kai dala tiriliyan 7.7, tare da faɗaɗa tattalin arzikin Nijeriya. TRT Hausa Tinubu, ta bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya ce shirin na nuna aniyar Nijeriya ta shiga kasuwar halal ta duniya, inda ake sa ran zai ƙara kusan dala biliyan 1.5 ga tattalin arzikin ƙasar nan da shekarar 2027. TRT Hausa Tsarin zai mayar da hankali kan faɗaɗa fitar da abinci mai bin ƙa’idar halal, bunƙasa masana’antar magunguna da kayan kwalliya, inganta yawon buɗe ido na halal, da samar da hanyoyin kuɗi masu ɗa’a, tare da hasashen samar da darajar tattalin arziki da ta haura dala biliyan 12 nan da 2030. TRT Hausa Gwamnatin Tarayya ta ce tattalin arzikin halal ba addini kaɗai ba ne, illa kasuwa ta duniya da ke mai da hankali kan inganci da tsaro, tare da taimakawa manufofin jawo jarin waje, faɗaɗa fitar da kayayyaki, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa. TRT Hausa