Sabuwar yarjejeniya za ta kara karfafa cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa ta soke harajin kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), yayin da ita ma UAE ta soke harajin kayayyaki 7,315 da ake kai wa kasar daga Nijeriya. Kasashen biyu sun dauki wannan matakin ne bayan sun cimma wata yarjejeniya ta bunkasa kasuwanci mai suna Nigeria–UAE Comprehensive Economic Partnership Agreement wadda aka sanya wa hannu a watan Janairun 2026. Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Nijeriya ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta kara karfafa harkokin kasuwanci, tare da samar da sabbin damarmakin zuba jari da fadada cinikayya tsakanin kasashen biyu. A karkashin yarjejeniyar, Nijeriya ta cire haraji kan kayayyaki 3,949 wanda ya kai kashi 63.3 cikin dari na jimillar kayayyakin. Bugu da kari, a baya Nijeriya ta riga ta cire haraji kan wasu kayayyaki 2,294 cikin shekaru biyar da suka gabata, inda yanzu kayayyaki 123 kacal suka rage da ba a cire harajinsu ba. A nata bangaren, UAE ta cire haraji kan kayayyaki 2,805, wanda ya kai kashi 38.3 cikin dari na dukkan kayayyakin. Haka kuma za ta cire haraji kan kayayyaki 1,468 cikin shekaru uku masu zuwa, sannan kuma ta cire na wasu kayayyaki 3,042 a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Nijeriya, Jumoke Oduwole, tare da Ministan Kasuwanci da Harkokin Waje na UAE, Dr. Thani bin Ahmed Al Zeyoudi, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a gaban Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da Shugaban UAE Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan. Tushen labari: Newstimehub
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Nijeriya da UAE sun soke haraji kan dubban kayayyaki domin bunkasa kasuwanci
Sabuwar yarjejeniya za ta kara karfafa cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa ta soke harajin kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), yayin da ita ma UAE ta soke harajin kayayyaki 7,315 da ake kai wa kasar daga Nijeriy...
At a glance
Sabuwar yarjejeniya za ta kara karfafa cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa ta soke harajin kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), yayin da ita ma UAE ta soke harajin kayayyaki 7,315 da ake kai wa kasar daga Nijeriy...
