Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Nijeriya da Nijar sun ƙulla yarjejeniya kan tsaron iyaka da kasuwanci

Kwastam na ƙasashen biyu sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki Hukumar Kwastam ta Nijeriya da Gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun cimma yarjejeniya ta dabarun haɗin gwiwa kan tsaron iyaka, kare kayayyakin da ke wucewa ta iyakoki da kuma bunƙasa hulɗar tattalin arziƙi tsak...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:18
Nijeriya da Nijar sun ƙulla yarjejeniya kan tsaron iyaka da kasuwanci
Em resumo

Kwastam na ƙasashen biyu sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki Hukumar Kwastam ta Nijeriya da Gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun cimma yarjejeniya ta dabarun haɗin gwiwa kan tsaron iyaka, kare kayayyakin da ke wucewa ta iyakoki da kuma bunƙasa hulɗar tattalin arziƙi tsak...

Kwastam na ƙasashen biyu sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki Hukumar Kwastam ta Nijeriya da Gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun cimma yarjejeniya ta dabarun haɗin gwiwa kan tsaron iyaka, kare kayayyakin da ke wucewa ta iyakoki da kuma bunƙasa hulɗar tattalin arziƙi tsakanin ƙasashen biyu. TRT Hausa Babban Kwanturola Janar na Kwastam ta Nijeriya, Bashir Adeniyi, ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawar haɗin gwiwa da aka gudanar a Abuja, inda tawagar Kwastam ta Nijar ke ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Muhammadu Yaqouba. TRT Hausa Adeniyi ya ce haɗin gwiwar za ta mayar da hankali kan sauƙaƙa kasuwancin yankin, kare kayayyakin da ke wucewa, musayar bayanai da kuma inganta tsaro a kan iyakokin ƙasashen biyu. TRT Hausa Ya bayyana cewa an tsara yarjejeniyar ne domin inganta jigilar kayayyaki zuwa Nijar ta hanyar Nijeriya, rage jinkiri a hanyoyin wucewa da kuma magance matsalolin tsaro, domin kasuwanci na halal ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen biyu. TRT Hausa Babban Kwanturola Janar ɗin ya amince cewa ƙasashen da ba su da tashar ruwa na fuskantar ƙalubale, yana mai jaddada cewa Nijeriya za ta ci gaba da tallafa wa Nijar da sauran maƙwabta wajen sauƙaƙa kasuwanci, duk da bambance-bambancen siyasa. TRT Hausa Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da kafa hanyoyin tsaro na musamman da izinin wucewa cikin aminci domin sauƙaƙa zirga-zirgar manyan motocin kaya a kan iyakoki. TRT Hausa