Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Nijeriya da China sun ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da makamashin nukiliya

Nijeriya da China sun kwashe tsawon shekara 50 suna hulɗar diflomasiyya, sannan sun daɗa ƙarfafa ɗangantaka a shekarar 2018 bayan haɗin gwiwarsu a shirin kasuwanci na Belt and Road initiative. Nijeriya da China sun ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da raya albarkatun ɗan' adam da kuma makamashin nukil...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:18
Nijeriya da China sun ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da makamashin nukiliya
Кратко

Nijeriya da China sun kwashe tsawon shekara 50 suna hulɗar diflomasiyya, sannan sun daɗa ƙarfafa ɗangantaka a shekarar 2018 bayan haɗin gwiwarsu a shirin kasuwanci na Belt and Road initiative. Nijeriya da China sun ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da raya albarkatun ɗan' adam da kuma makamashin nukil...

Nijeriya da China sun kwashe tsawon shekara 50 suna hulɗar diflomasiyya, sannan sun daɗa ƙarfafa ɗangantaka a shekarar 2018 bayan haɗin gwiwarsu a shirin kasuwanci na Belt and Road initiative. Nijeriya da China sun ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da raya albarkatun ɗan' adam da kuma makamashin nukiliya a ganawar da shugabannin ƙasashen biyu suka yi gabannin soma babban taron haɗin gwiwar China da Afirka a ranar Laraba, a cewar mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya. China, ita ce ƙasa mafi girma wadda ke baiwa Nijeriya lamuni, inda a ƙarshen watan Maris bashin da take bin ƙasar ya kai dala biliyan 5, kamar yadda alƙaluman ofishin kula da basussuka a Nijeriya suka bayyana. Ƙasashen biyu dai, sun kwashe tsawon shekara 50 suna hulɗar diflomasiyya, sannan sun ɗaɗa karfafa ɗangantakarsu a shekarar 2018 bayan haɗin gwiwarsu a shirin kasuwanci na Belt and Road initiative. Haɗin gwiwar dai, ta samar da manyan ayyukan more rayuwa a Nijeriya tun daga tashar ruwa mai zurfi zuwa ga layin dogo. "Akwai buƙatar wannan gagarumin haɗin gwiwar ta samar da ingantacciyar ci gaba da daidaito da kuma tsaro a yankin na Yammacin Afirka, '' in ji Shugaba Tinubu a ranar Talata. Shugaba Tinubu na daga cikin shugabannin kasashen Afirka 50 da suka isa birnin Beijing a wannan makon domin halartar babban taron haɗin gwiwar China da Afirka na shekarar 2024 wanda shugaba ƙasar Xi Jinping ya kira a matsayin wata dama ta ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin China da Afirka. "China da Nijeriya, a matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa, suna karfafa haɗin gwiwarsu a manyan tsare-tsare, waɗanda za su taimaka wajen kara kaimi a dangantakar dake tsakanin China da Afirka da kuma buɗe hanyoyin samar da ci gaba a tsakanin kasashen duniya." in ji shugaba Xi kasashen biyu sun amince su inganta haɗin gwiwa a fannin hada-hadar kuɗi kamar musayar kuɗin ƙasashen biyu don inganta harkokin cinikayya a tsakani, kamar yadda kamfanin dillancin labaran China ta rawaito shugaba Xi ya ce. Har ilau sun amince su haɗa kai a kan bayanan sirri don yaki da safarar kuɗaɗe da ba da tallafi ga 'yan ta'adda. A yayin ziyarar dai, shugaba Tinubu ya samu damar zuwa ɗakin bincike na kamfanin Huawei inda aka yi mishi alƙawarin samar da dakin gwaje-gwaje na kasken rana na haɗin gwiwa a Nijeriya Kazalika, wani kamfanin China ya yi alƙawarin kafa cibiyar haɗa motoci masu amfani da wutar lantarki da kuma horar da 'yan NIjeriya fasahar kere-kere da bunkasa makamashin da ake sabunta su.