Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Nijar ta yanke hulɗar jakadanci da Ukraine kan zargin ta'addanci

Kakakin gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Amadou Abdramane ne ya bayyana da ɗaukar matakin ranar Talata a wata sanarwa da ya karanto ta gidan talbijin na ƙasar. Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da yanke hulɗar jakadanci da Ukraine "nan-take", bayan sun zargi ƙasar da goyon bayan "ƙungi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:18
Nijar ta yanke hulɗar jakadanci da Ukraine kan zargin ta'addanci
De un vistazo

Kakakin gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Amadou Abdramane ne ya bayyana da ɗaukar matakin ranar Talata a wata sanarwa da ya karanto ta gidan talbijin na ƙasar. Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da yanke hulɗar jakadanci da Ukraine "nan-take", bayan sun zargi ƙasar da goyon bayan "ƙungi...

Kakakin gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Amadou Abdramane ne ya bayyana da ɗaukar matakin ranar Talata a wata sanarwa da ya karanto ta gidan talbijin na ƙasar. Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da yanke hulɗar jakadanci da Ukraine "nan-take", bayan sun zargi ƙasar da goyon bayan "ƙungiyoyin 'yan ta'adda" Kakakin gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Amadou Abdramane ne ya bayyana da ɗaukar matakin ranar Talata a wata sanarwa da ya karanto ta gidan talbijin na ƙasar. Ya ƙara da cewa za su shaida wa Majalisar Ɗinkin Duniya wannan lamari domin ta tattauna kan "kutsen" da Ukraine take yi a ƙasarsu. Nijar ta yanke hulɗar jakadanci da Ukraine ne kwana biyu bayan maƙociyarta Mali ta sanar da daukar irin wannan mataki, sakamakon zargin da ta yi wa mahukuntan birnin Kiev na hannu a hare-haren da 'yan ta'adda suka kai wa sojojinta inda suka kashe da dama daga cikinsu a kwanakin baya.