Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Nijar ta sa hannu kan kundin tattara bayanan 'yan ta'adda

Dokar ta tanadi hukuncin karɓe takardar shaidar ɗan ƙasa ga duk wanda aka sanya sunansa a kundin, sannan idan aka yanke wa mutum hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar ko fiye da haka za a ƙwace shaidarsa ta ɗan ƙasa dindindin. Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sa hannu a wata doka ta ku...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:18
Nijar ta sa hannu kan kundin tattara bayanan 'yan ta'adda
At a glance

Dokar ta tanadi hukuncin karɓe takardar shaidar ɗan ƙasa ga duk wanda aka sanya sunansa a kundin, sannan idan aka yanke wa mutum hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar ko fiye da haka za a ƙwace shaidarsa ta ɗan ƙasa dindindin. Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sa hannu a wata doka ta ku...

Dokar ta tanadi hukuncin karɓe takardar shaidar ɗan ƙasa ga duk wanda aka sanya sunansa a kundin, sannan idan aka yanke wa mutum hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar ko fiye da haka za a ƙwace shaidarsa ta ɗan ƙasa dindindin. Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sa hannu a wata doka ta kundin tattara bayanan 'yan ta'adda, wadda za ta taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da ta'addaci da kuma ayyukan da ke barazana ga tsaron ƙasar. Dokar wadda shugaban ƙasar Birgediya Janar Abdurahamane Tiani ya sanya wa hannu a ranar 27 ga watan Agustan 2024 ta tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda aka samu da laifi. Hukumomin Nijar dai sun ƙirƙiro kundin ne don rajistar bayanan duk wani mutum ko wata ƙungiya da ke da hannu a ayyukan ta'addanci. Daga yanzu, za a riƙa yin rajistar duk wani ɗan ta’adda da ke da alaƙa da ayyukan ta’addanci a cikin kundin na ƙasa sannan za a karɓe shaidar mutum na ɗan kasa na wani ɗan lokaci ko na dindindin tare da sauran wasu hukunce-hukunce masu tsauri kana kwamitin tattara bayanai na ƙasa shi zai na sa ido a kan dokar. Takunkumi Duk wani mutum ko ƙungiya ko ma'aikata da bayanansu suka shiga cikin kundin, za a hana su yin balaguro a cikin ƙasar har ma da ƙasashen waje tare da sanya takunkumi a hada-hadar kasuwanci da kuma rufe kadarorinsu. Kazalika, hukuncin ya tanadi karɓe takardar shaidar ɗan ƙasa sannan idan aka yanke wa mutum hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar ko fiye da haka za a kwace shaidarsa ta ɗan kasa na dindindin. Wannan sabon tsarin dai na zama wani gagarumin mataki a ƙoƙarin da gwamnatin Nijar ke yi na kawar da barazanar tsaro tare da samar da zaman lafiya a ƙasar wadda ke yankin Yammancin Afirka.