Anelka ya kasance dan wasan da ya fi zura ƙwallaye a Gasar Premier da ƙwallo 19 a kakar wasa tsakanin shekarar 2008 zuwa 2009 a matsayin dan wasan Chelsea. Wata kungiyar kwallon kafa ta kasar Turkiyya ta dauki tsohon dan wasan Faransa Nicolas Anelka aiki a matsayin kocinta a ranar Alhamis. “Maraba, Farfesa! Kulob ɗinmu ya amince da Nicolas Anelka a matsayin shugaba, kamar yadda kungiyar kwallon kafa ta Umraniyespor da ke Istanbul wadda a halin yanzu take rukuni na biyu na Turkiyya, ta wallafa a shafinta na X. Umraniyespor ta sauka kasan teburi Gasar Super Lig a kakar wasan bara. Anelka, mai shekara 44, ya kasance tsohon dan wasan Faransa kuma ya buga wasa a manyan fitattatun kungiyoyin kwallon kafa na Turai kamar Paris Saint-Germain da Arsenal da Real Madrid da Liverpool da Manchester City da Chelsea da kuma Juventus. Tauraron na daya daga cikin manyan 'yan wasan kwallon kafa a zamaninsa sannan gwarzo ne da ya taka muhimmiyar rawa a tsakanin 'yan wasa a Gasar Premier ta Ingila. Anelka ya shafe kaka daya da rabi a kungiyar Fenerbahce da ya zama zakaran Turkiyya a shekara ta 2005. A shekarar 2016 ne ya yi ritaya daga buga kwallon kafa bayan ya buga wasa a birnin Mumbai na kasar Indiya. Anelka ya kasance ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a Gasar Premier da ƙwallaye 19 a kakar wasa ta shekarar 2008 zuwa 2009 a matsayin dan wasan Chelsea. Ya lashe gasar Zakarun Turai lokacin yana Real Madrid a shekara ta 2000, kafin ya taimaka wa Faransa ta lashe kofin EURO ta 2000. Anelka ya kasance zakaran gasar Ingila sau biyu, a kungiyar Arsenal a shekarar 1998 da Chelsea a shekarar 2010. Daga karshe ya jagoranci wata karamar kungiyar kwallon kafa ta Faransa Hyeres a shekarar 2021 bayan horar da kungiyar matasa ta Lille.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Nicolas Anelka ya zama koci a wata kungiyar kwallon kafar Turkiyya
Anelka ya kasance dan wasan da ya fi zura ƙwallaye a Gasar Premier da ƙwallo 19 a kakar wasa tsakanin shekarar 2008 zuwa 2009 a matsayin dan wasan Chelsea. Wata kungiyar kwallon kafa ta kasar Turkiyya ta dauki tsohon dan wasan Faransa Nicolas Anelka aiki a matsayin kocinta a ranar Alhamis. “Marab...

Anelka ya kasance dan wasan da ya fi zura ƙwallaye a Gasar Premier da ƙwallo 19 a kakar wasa tsakanin shekarar 2008 zuwa 2009 a matsayin dan wasan Chelsea. Wata kungiyar kwallon kafa ta kasar Turkiyya ta dauki tsohon dan wasan Faransa Nicolas Anelka aiki a matsayin kocinta a ranar Alhamis. “Marab...
