Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Netanyahu yana sukar Turkiyya ne domin ɓoye laifukan da yake aikatawa: Altun

A yayin da wasu shugabanni suke son wanzar da zaman lafiya da tsaro, wasu kuwa, irin su Netanyahu, sun fifita rashin imani da rashin mutunci da tayar-da-zaune-tsaye, a cewar daraktan sadarwa na Turkiyya. Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya caccaki Firaiministan Isra'ila Benjamin Netan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:18
Netanyahu yana sukar Turkiyya ne domin ɓoye laifukan da yake aikatawa: Altun
Kwa muhtasari

A yayin da wasu shugabanni suke son wanzar da zaman lafiya da tsaro, wasu kuwa, irin su Netanyahu, sun fifita rashin imani da rashin mutunci da tayar-da-zaune-tsaye, a cewar daraktan sadarwa na Turkiyya. Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya caccaki Firaiministan Isra'ila Benjamin Netan...

A yayin da wasu shugabanni suke son wanzar da zaman lafiya da tsaro, wasu kuwa, irin su Netanyahu, sun fifita rashin imani da rashin mutunci da tayar-da-zaune-tsaye, a cewar daraktan sadarwa na Turkiyya. Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya caccaki Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bisa ci gaba da yin amfani da dabarun yaudara domin janye hankalin duniya daga laifukan da ake zarginsa da aikatawa. Altun ya bayyana haka ne a saƙon da ya wallafa a shafin X ranar Asabar, yana mai cewa babu wata yaudara ta Netanyahu da za ta sa tarihi ya manta da ɓarnar da gwamnatinsa take aikatawa a kan fararen-hular da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza, inda ya bayyana shi a matsayin abin kunya ga ƙasarsa. "Netanyahu ya sake sukar ƙasarmu domin ya ɓoye laifukan da yake aikatawa. Babu wata ƙarya da yaudara da za ta ɓoye kisan ƙare-dangin da ya yi wa fararen-hular da ba su da laifi. Tuni aka sani cewa shi ne shugaban da ya fi rashin imani da aka taɓa samu a wannan yanki da ma ƙasarsa," in ji Altun. Altun ya ce akwai shugabannin da ke ƙaunar zaman lafiya da tabbatar da tsaro irin su Shugaba Recep Tayyip Erdogan waɗanda suka sanya walwalar ƴan ƙasarsu da ta maƙwabtansu a gaba kuma ya kamata a yi koyi da su. Ya jaddada manufofin Erdogan na kare gaskiya da yin adalci a duniya baki ɗaya, yana mai fito da muhimancin adalci daga shugabanni.