Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Netanyahu ya amince da tattaunawar tsagaita wuta ta Gaza a Qatar da Masar

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 175 tana yi a yankin Gaza da ta mamaye, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 32,552 sannan ta jikkata fiye da mutum 74,980 a yayin da Kotun Duniya ta umarce ta da ta daina jefa Gaza cikin bala'in yunwa. 1300 GMT — Netanyahu ya amince da tattaunawar tsagaita w...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:18
Netanyahu ya amince da tattaunawar tsagaita wuta ta Gaza a Qatar da Masar
At a glance

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 175 tana yi a yankin Gaza da ta mamaye, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 32,552 sannan ta jikkata fiye da mutum 74,980 a yayin da Kotun Duniya ta umarce ta da ta daina jefa Gaza cikin bala'in yunwa. 1300 GMT — Netanyahu ya amince da tattaunawar tsagaita w...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 175 tana yi a yankin Gaza da ta mamaye, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 32,552 sannan ta jikkata fiye da mutum 74,980 a yayin da Kotun Duniya ta umarce ta da ta daina jefa Gaza cikin bala'in yunwa. 1300 GMT — Netanyahu ya amince da tattaunawar tsagaita wuta ta Gaza a Doha da Alkahira Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya amince da aikewa da tawaga zuwa Masar da Qatar, inda masu shiga tsakani ke kokarin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, in ji ofishinsa. Ofishin Netanyahu ya ce ya yi magana da shugabannin hukumomin leken asirin Isra'ila Shin Bet da Mossad kuma "ya amince da cewa tawagogi a madadinsu za su tafi Doha da Alkahira a cikin kwanaki masu zuwa," tare da ba da umarnin ci gaba da yin shawarwari. 0929 GMT — Isra'ila ta hana Falasɗinawa shiga Masallacin Ƙudus a ranar Juma'a 3 ga watan Ramadan Hukumomin Isra'ila sun hana Falasɗinawa daga Gabar Yamma da Kogin Jordan shiga Masallacin Ƙudus da ke Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye a ranar Juma'a ta uku a jere na watan Ramadan. Sojojin Isra'ila sun jibge dakarunsu a mashigar Birnin Ƙudus, inda suka binciki ko wane ne Falasɗinawa tare da hana wasu daga cikinsu shiga, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa Anadolu. Mashigar Qalandia a Arewacin Kudus da wurin bincike na "300" a kudancin birnin sun shaida tuttuɗar jama'a sosai a ƙofofin shiga daga Yammacin Kogin Jordan zuwa Kudus. Rundunar ta ƙara da cewa mazan da suka haura shekaru 55 da mata ƴan sama da shekaru 50, da yara ‘yan kasa da shekaru 10 ne kadai za a ba su izinin shiga Birnin Ƙudus. Sabbin matakan dai ba su hada da mazauna Gaza ba, inda hukumomin Isra'ila suka hana shiga Birnin Ƙudus sai da izini na musamman. 0415 GMT — Amurka na so a yi bincike kan bidiyon da ya nuna sojojin Isra'ila suna binne mutane da ransu Amurka ta ce ta yi matuƙar "damuwa" da ganin wani bidiyo wanda ya nuna dakarun Isra'ila sun harbi Falasɗinawa biyu da ba su ɗauke da makami sannan suka binne su da katafila, inda ta yi kira a gudanar da bincike. A yayin da aka tambaye shi game da bidiyon, kakakin Ma'aikatar Tsaron Amurka ya shaida wa Anadolu cewa ba su tantance sahihancin bidiyon ba, yana mai ƙarawa da cewa za su yi gaggawar neman ƙarin bayani daga gwamnatin Isra'ila. "Muna sa rai za a yi cikakken bincike game da wannan batu, idan kuma aka gano gaskiya nem a ɗauki mataki," in ji mai magana da yawun ma'aikatar tsaron ta Amurka. "Kazalika, mun bayyana ƙarara cewa wajibi ne ga Isra'ila ta gudanar da bincike game da zarge-zargen da ake yi mata na keta dokokin yaƙi, sannan ta tabbatar da adalci da kuma ɗaukar matakai na hana sake aukuwar hakan," a cewarsa. Wani bidiyo da sashen Larabci na gidan talbijin na Al Jazeera ya watsa ya nuna mutanen biyu suna tafiya a sarari a gaɓar tekun Gaza inda suka riƙa ɗaga fararen ƙyallaye da ke nuna zaman lafiya kafin sojojin Isra'ila su kashe su. 0217 GMT — 'Yan Houthi na Yemen sun kai hari kan jiragen ruwa 86 tun farkon yaƙin Gaza Kungiyar Houthi ta Yemen ta ce ta kai hari kan jiragen ruwa 86 a tekun Bahar Maliya, Tekun Arabiya, da Tekun Indiya da ke da alaka da Isra'ila, Amurka da Birtaniya tun bayan yakin Gaza da Isra'ila ta fara a watan Oktoban bara. A wani jawabi da ya yi ta tashar talabijin ta Al Masirah, shugaban 'yan Houthi Abdulmalik Al Houthi ya ce sojojin ruwan kasar Yemen da ke da alaka da kungiyar, ya yi nuni da cewa, sun kai hari kan jiragen ruwa guda tara a cikin wannan mako. Al Houthi ya ce a cikin hare-hare 10 da aka gudanar a tsawon mako guda, sun yi amfani da makamai masu linzami 37 da jirage marasa matuka, ya kara da cewa, kungiyar ta kuma kai hare-hare da makamai masu linzami a wurare da dama a birnin Eilat na kudancin Isra'ila. Da yake jaddada raguwar zirga-zirgar jiragen ruwa da Isra'ila ke yi a Tekun Bahar Rum, ya yi gargadin cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukansu idan har aka ci gaba da kai hare-hare a Gaza.