An ƙwace kilo 30.09 na hodar iblis da wasu manyan miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama wata ’yar ƙasar Brazil mai shekaru 30, Imgrid Benevides, dauke da kilogram 30.09 na hodar iblis a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. An ɓoye hodar iblis ɗin ne a cikin mazubin gahawa, kuma an kama ta bayan ta iso Nijeriya ta jirgin Qatar Airways. TRT Hausa NDLEA ta ce Benevides jami’ar tsaro ce a Brazil, kuma an sanya ido a kanta kafin kama ta. Hukumar ta bayyana cewa wannan shi ne mafi girman kamen hodar iblis da aka taba yi a lokaci guda, bayan gwaji ya tabbatar da cewa kayan da aka ɓoye ba gahawa ba ce illa hodar iblis mai yawa. TRT Hausa A wani samame a filin jirgin Murtala Mohammed da ke Legas, NDLEA ta kama wasu mutane biyu yayin da suke shirin tafiya Istanbul, Turkiyya, dauke da kwayoyi 3,990 na tapentadol da tramadol da aka boye cikin kayan abinci a jakunkunansu. TRT Hausa Hukumar ta kuma kama wani jirgin ruwa a gabar Lekki dauke da buhuna 44 na tabar wiwi da aka shigo da su daga Ghana, masu nauyin kilogram 1,848. Haka zalika a Kaduna, jami’an NDLEA sun kama wasu matasa biyu dauke da abubuwan fashewa guda 140 a yayin binciken ababen hawa a kan hanyar Zaria–Kaduna. TRT Hausa
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
NDLEA Ta Kama ’Yar Brazil da Hodar Iblis a Filin Jirgin Abuja
An ƙwace kilo 30.09 na hodar iblis da wasu manyan miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama wata ’yar ƙasar Brazil mai shekaru 30, Imgrid Benevides, dauke da kilogram 30.09 na hodar iblis a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abu...

An ƙwace kilo 30.09 na hodar iblis da wasu manyan miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama wata ’yar ƙasar Brazil mai shekaru 30, Imgrid Benevides, dauke da kilogram 30.09 na hodar iblis a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abu...
