الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben Kodin kusan 100,000

Hukumar ta ce ta kuma kama wata dattijuwa mai shekara 70 tare da danta da kilo 117.900 na wiwi. Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce ta yi kamen miyagun kwayoyi masu dumbin yawa daf da Bikin Kirisimeti. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:18 ص
NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben Kodin kusan 100,000
لمحة سريعة

Hukumar ta ce ta kuma kama wata dattijuwa mai shekara 70 tare da danta da kilo 117.900 na wiwi. Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce ta yi kamen miyagun kwayoyi masu dumbin yawa daf da Bikin Kirisimeti. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta...

Hukumar ta ce ta kuma kama wata dattijuwa mai shekara 70 tare da danta da kilo 117.900 na wiwi. Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce ta yi kamen miyagun kwayoyi masu dumbin yawa daf da Bikin Kirisimeti. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa daga cikin miyagun kwayoyin da ta kama har da kwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben maganin tari mai dauke da kodin kusan 100,000. Hukumar ta ce ta kama kwayoyin na Tramadol a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas tare da da hadin gwiwa da jami’an kwastam da sauran jami’an tsaro. Hukumar ta ce an shigo da kwayoyin ne daga birnin Hamburg na Jamus. A cewar sanarwar, kwayoyin na cikin manyan kwalaye 100 wadanda baki dayansu nauyinsu ya kai kilo 7,150. NDLEA intercepts 7.5m tramadol pills, 95,400 codeine bottles Christmas consignments . Arrests 70-year-old grandma, her son for drug trafficking as Agencys sniffer dogs uncover cocaine in India-bound shipment Read more at: https://t.co/RBSMr9FNq2 pic.twitter.com/eTjvsopFVd — NDLEA NIGERIA (@ndlea_nigeria) December 24, 2023 Haka kuma hukumar ta ce jami’anta da ke aiki a Legas sun kai wani samamen a wasu shaguna biyu a ranar Laraba 20 ga watan Disamba a kasuwar duniya da ke yankin Ojo. NDLEA ta ce bayan sun yi bincike sai suka gano kwali 258 na maganin tari na ruwa mai dauke da kodin da kuma kwali takwas na kodin din amma na kwaya. Kwalayen na dauke da kwalabe 49,200 na maganin tarin na ruwa sai kuma kwayoyi 46,200. Hukumar ta ce washe gari jami’an hukumar sun kai samame a wani gida a unguwar Mushin ta ke jihar ta Legas inda suka kama wata dattijuwa mai shekara 70 mai suna Selifat Funke Cole da danta Babajide Ayorinde Cole inda aka kama su da kilo 117.900 na wiwi.