Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

NAFDAC ta rufe wani kamfani mai 'samar da jabun' kayan kwalliya a Legas

Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen sayen kayan kwalliya tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa. Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta rufe wata haramtacciyar masana’anta da ke samar da jabun kayan kwalliya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:18
NAFDAC ta rufe wani kamfani mai 'samar da jabun' kayan kwalliya a Legas
A taƙaice

Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen sayen kayan kwalliya tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa. Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta rufe wata haramtacciyar masana’anta da ke samar da jabun kayan kwalliya...

Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen sayen kayan kwalliya tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa. Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta rufe wata haramtacciyar masana’anta da ke samar da jabun kayan kwalliya a rukunin shagunan Benue Plaza da ke Filin Bajekoli a jihar Legas da ke kudancin ƙasar. NAFDAC ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, inda ta ce an rufe masana’antar ne bayan da jami’anta suka kai samame tare da gano wasu sinadarai da kayayyakin da ba su da rajista, da kuma waɗanda lokacin amfani da su ya wuce suka lallace. A yayin gudanar da aikin, hukumar ta NAFDAC ta kama fiye da kwali 1,200 na kayan kwalliya na jabu. NAFDAC Shuts Down Illegal Cosmetics Factory in Lagos State. NAFDAC has shut down an illegal factory producing counterfeit cosmetic products at Benue Plaza, Trade Fair Complex in Lagos State. pic.twitter.com/Xko4lNfQSe — NAFDAC NIGERIA (@NafdacAgency) September 17, 2024 Kayayyakin sun hada da kananan mazubai na haɗe-haɗe, da sinadarai marasa tambari da ma wasu na'urori, inda aka ƙwace aka kai su ofishin NAFDAC domin ci gaba da bincike. “Hukumar ta ƙiyasta darajar kayayyakin da aka ƙwace a farashin kan titi inda ya kai kusan naira miliyan 50,” in ji NAFDAC. Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen sayen kayan kwalliya tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa.