الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

NAFDAC na son a fara yanke hukuncin kisa ga masu safarar jabun magunguna a Nijeriya

“Wani ya sayi magungunan yara kan N13,000, wani kuma yana sayar da shi N3,000 a cikin rukunin shaguna ɗaya,” kamar yadda shugabar ta NAFDAC ta bayyana a ranar Juma’a. Hukumar NAFDAC wadda ke kula da ingancin abinci da magunguna ta buƙaci a fara yanke hukuncin kisa ga waɗanda ke safarar jabun magu...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:18 ص
NAFDAC na son a fara yanke hukuncin kisa ga masu safarar jabun magunguna a Nijeriya
لمحة سريعة

“Wani ya sayi magungunan yara kan N13,000, wani kuma yana sayar da shi N3,000 a cikin rukunin shaguna ɗaya,” kamar yadda shugabar ta NAFDAC ta bayyana a ranar Juma’a. Hukumar NAFDAC wadda ke kula da ingancin abinci da magunguna ta buƙaci a fara yanke hukuncin kisa ga waɗanda ke safarar jabun magu...

“Wani ya sayi magungunan yara kan N13,000, wani kuma yana sayar da shi N3,000 a cikin rukunin shaguna ɗaya,” kamar yadda shugabar ta NAFDAC ta bayyana a ranar Juma’a. Hukumar NAFDAC wadda ke kula da ingancin abinci da magunguna ta buƙaci a fara yanke hukuncin kisa ga waɗanda ke safarar jabun magunguna. Daraktar hukumar Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka inda ta ce ya kamata a ɗauki wannan mataki musamman sakamakon yadda irin waɗannan magungunan ke jawo mutuwar yara, kamar yadda ta shaida wa gidan talabijin na Channels a ƙasar. “Wani ya sayi magungunan yara kan N13,000, wani kuma yana sayar da shi N3,000 a cikin rukunin shaguna ɗaya,” kamar yadda shugabar ta NAFDAC ta bayyana a ranar Juma’a. Shugabar ta NAFDAC ta bayyana cewa babu wasu sinadaren magance cuta da aka gani a cikin maganin bayan an gudanar da gwaji a kan maganin a ɗaya daga cikin ɗakunan gwajin na hukumar da ke Kaduna. Hukumar ta NAFDAC ta bayyana cewa tana neman a samu goyon bayan ɓangaren shari’a domin su bayar da goyon baya kan hakan. Ta bayyana cewa hukumar na aiki tare da ‘yan majalisa domin ganin haƙarsu ta cim ma ruwa.