Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Hatsarin helikwaftar asibiti ya kashe mutane biyar a Libya

Jirgin ya faɗi ne bayan aikin kuɓutar da mara lafiya kusa da Kufra Wani helikwafta na asibiti ya yi hatsari a sansanin Al-Sarra na Libya yayin da yake sauka bayan kammala aikin kuɓutar da mara lafiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, kamar yadda kafafen watsa labaran ƙasar suka ruwa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:18
Hatsarin helikwaftar asibiti ya kashe mutane biyar a Libya
Bu haberde ne var?

Jirgin ya faɗi ne bayan aikin kuɓutar da mara lafiya kusa da Kufra Wani helikwafta na asibiti ya yi hatsari a sansanin Al-Sarra na Libya yayin da yake sauka bayan kammala aikin kuɓutar da mara lafiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, kamar yadda kafafen watsa labaran ƙasar suka ruwa...

Jirgin ya faɗi ne bayan aikin kuɓutar da mara lafiya kusa da Kufra Wani helikwafta na asibiti ya yi hatsari a sansanin Al-Sarra na Libya yayin da yake sauka bayan kammala aikin kuɓutar da mara lafiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, kamar yadda kafafen watsa labaran ƙasar suka ruwaito. TRT Hausa Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne ranar Litinin, kimanin kilomita 300 daga birnin Kufra a kudu maso gabashin Libya. Daga cikin waɗanda suka mutu akwai mambobin rundunar sufuri ta soji biyu, wani ma’aikacin jinya daga Kufra, da kuma matuƙin jirgin da mataimakinsa waɗanda ‘yan ƙasashen waje ne. TRT Hausa Kafafen watsa labarai sun bayyana cewa helikwaftar na aikin kuɓutarwa ne bayan wani soja ya jikkata a wani hatsari a yankin hamada, kuma duk da isowar jami’an gaggawa da wuri, babu wanda ya tsira daga cikin waɗanda ke cikin jirgin. TRT Hausa