Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Mutane sun yi wawason kayan abinci daga ma'ajiyar gwamnati a Abuja

Wasu mutane a Abuja babban birnin Nijeriya sun daka wawaso kan wata ma'ajiyar kayan abinci ta gwamnati ranar Lahadi. Wasu mutane sun yi wawason kayan abinci da ke ajiye a wani rumbun gwamnati da ke birnin tarayya Abuja, ranar Lahadi. Ma'ajiyar mallakin hukumar ba da tallafin gaggawa ce ta NEMA. J...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:18
Mutane sun yi wawason kayan abinci daga ma'ajiyar gwamnati a Abuja
En bref

Wasu mutane a Abuja babban birnin Nijeriya sun daka wawaso kan wata ma'ajiyar kayan abinci ta gwamnati ranar Lahadi. Wasu mutane sun yi wawason kayan abinci da ke ajiye a wani rumbun gwamnati da ke birnin tarayya Abuja, ranar Lahadi. Ma'ajiyar mallakin hukumar ba da tallafin gaggawa ce ta NEMA. J...

Wasu mutane a Abuja babban birnin Nijeriya sun daka wawaso kan wata ma'ajiyar kayan abinci ta gwamnati ranar Lahadi. Wasu mutane sun yi wawason kayan abinci da ke ajiye a wani rumbun gwamnati da ke birnin tarayya Abuja, ranar Lahadi. Ma'ajiyar mallakin hukumar ba da tallafin gaggawa ce ta NEMA. Josephine Adeh, wata jami'ar hukumar a Abuja ta tabbatar da faruwar lamarin ga kafafen watsa labarai, ko da yake ta ce an "shawo kan" lamarin. A safiyar Lahadi ne mutane suka kai hari kan ma'ajiyar da ke unguwar Karimo a yankin Abuja Phase 3. Jami'an 'yan sanda da aka jibge a ma'ajiyar sun samu nasarar korar dandazon mutanen a cewar Adeh. Sai dai kuma, ba ta ambaci ko an gudanar da kame ba sakamakon faruwar lamarin. Zanga-zanga Nijeriya ta fuskanci yawaitar zanga-zanga kan tsadar rayuwa, inda fusatattun mutane ke zargin shugaban ƙasa Bola Tinubu da aiwatar da matakan da ke ƙuntatawa 'yan kasa, da suka haɗa da cire tallafin man fetur. Shugaban ya amsa cewa yana sane da matsin rayuwar da ke addabar 'yan Nijeriya, amma ya bayyana kyakkyawan fatansa kan ganin shirye-shiryen gwamnatinsa sun haifar da ɗa mai ido, inda ya ce tattalin arziƙin ƙasar zai inganta.