“Jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin kwantar da rikicin ta hanyar fesa tiyagas, sai kawai komai ya hargutse a cikin filin wasan inda aka yi ta ba-ta-kashi,” in ji jaridar Mediaguinee. Mutane da dama sun mutu yayin da gommai suka jikkata bayan wani rikici ya ɓarke ranar Lahadi yayin gasar ƙwallon ƙafa a kudu maso gabashin ƙasar Guinea, kamar yadda kafofin watsa labarai na ƙasar suka bayyana. Rikicin ya ɓarke ne bayan magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Labe sun ƙi amincewa da ƙwallon da ƙungiyar Nzerekore ta zura musu, lamarin da ya kai ga taho-mu-gama a Nzerekore, birni na biyu mafi girma a ƙasar, wanda ke da nisan kilomita kusan 570 daga Conakry, babban birnin ƙasar, a cewar jaridar Mediaguinee. Bayanai sun nuna cewa matakin da lafari ya ɗauka ne bai wa 'yan wasa biyu na Labe jan kati tare da bugun fenareti shi ne ya jawo rikicin. “Rikicin ya ɓarke ne yayin da magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafar suka riƙa jifa da duwatsu a cikin filin wasa. Jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin kwantar da rikicin ta hanyar fesa tiyagas, sai kawai komai ya hargitse a cikin filin wasan inda aka yi ta ba-ta-kashi,” in ji jaridar. Kawo yanzu gwamnati ta ba ce komai ba game da lamarin a hukumance. Amma rahotanni sun ce mutum fiye da 20 sun mutu, ciki har da ƙananan yara, a yayin da ake turmutsutsin fita daga filin wasan. “Mun fahimci cewa mutane da dama sun mutu, ciki har da ƙananan yara. A asibitin gunduma, an kwantar da mutane da dama da suka jikkata. Wasu daga cikin raunukan da suka ji munana ne," a cewar jaridar, wadda ta ambato wakilinta da ke yankin. Wasan da ake bugawa shi ne na ƙarshe a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa da Shugaban ƙasar Guinea Janar Mamady Doumbouya ke ɗaukar nauyi.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Mutane da dama sun mutu sakamakon rikicin da ya ɓarke a filin ƙwallon ƙafa a Guinea
“Jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin kwantar da rikicin ta hanyar fesa tiyagas, sai kawai komai ya hargutse a cikin filin wasan inda aka yi ta ba-ta-kashi,” in ji jaridar Mediaguinee. Mutane da dama sun mutu yayin da gommai suka jikkata bayan wani rikici ya ɓarke ranar Lahadi yayin gasar ƙwallon ƙafa a...

Bu haberde ne var?
“Jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin kwantar da rikicin ta hanyar fesa tiyagas, sai kawai komai ya hargutse a cikin filin wasan inda aka yi ta ba-ta-kashi,” in ji jaridar Mediaguinee. Mutane da dama sun mutu yayin da gommai suka jikkata bayan wani rikici ya ɓarke ranar Lahadi yayin gasar ƙwallon ƙafa a...
