Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Musulmai sun raba kwafin Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a Netherlands

An raba wa jama’a Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a ƙasar Netherlands a wani shiri na ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasar kan su riƙa karanta littafai masu tsarki maimakon ƙona su. An raba wa jama’a Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a ƙasar Netherlands a wani shiri na ƙarfafa gwiwar ’yan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:18
Musulmai sun raba kwafin Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a Netherlands
A taƙaice

An raba wa jama’a Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a ƙasar Netherlands a wani shiri na ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasar kan su riƙa karanta littafai masu tsarki maimakon ƙona su. An raba wa jama’a Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a ƙasar Netherlands a wani shiri na ƙarfafa gwiwar ’yan...

An raba wa jama’a Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a ƙasar Netherlands a wani shiri na ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasar kan su riƙa karanta littafai masu tsarki maimakon ƙona su. An raba wa jama’a Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a ƙasar Netherlands a wani shiri na ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasar kan su riƙa karanta littafai masu tsarki maimakon ƙona su. Shirin yana zuwa ne wata guda bayan jagoran kungiyar PEGIDA wanda ke kyamar Musulunci ya wulakanta Alkur’ani. Galip Aydemir, shugaban Gidauniyar Masallacin Arnhem Türkiyem wanda ke hadin gwiwa da Gidauniyar Dutch Diyanet ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa suna kokarin isar da sako ga jama’a kan abin da ya sa addinin Musulunci da Alkur’ani suke da daraja ga Musulmi. Muna so a samu hadin kai da ’yan uwantaka tsakanin mazauna birnin Arnhem,ya ce: “Ya kamata a daina kona Alkur’ani da sauran littafai masu tsarki, a rika karanta su ne.” John Maters, wani dan Netherlands wanda ya samu kwafin Alkur’anin ya yi godiya ga wadanda suka shirya taron kuma ya soki wadanda suka jagoranci wulakanta Alkur’ani a watan da ta gabata. “Abin da ya faru watan da ya gabata zai sa mutane su kara kin junansu ne. Ba na tunanin cewa sai mutumin da ya damu da addini zai fahimci cewa hakan rashin hankali ne,” in ji shi.