الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Murals: Masu zane-zane sun zayyana halin da Falasɗinawa ke ciki a kan titunan Nairobi na Kenya

Wasu matasa masu baiwar zane-zane sun zayyana yanayin kuncin da faladinawa suke ciki a kan titunan Nairobi babban birnin kasar Kenya domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza. Yakin da Isra'ila ke yi a yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya ya kashe mutan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:18 ص
Murals: Masu zane-zane sun zayyana halin da Falasɗinawa ke ciki a kan titunan Nairobi na Kenya
لمحة سريعة

Wasu matasa masu baiwar zane-zane sun zayyana yanayin kuncin da faladinawa suke ciki a kan titunan Nairobi babban birnin kasar Kenya domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza. Yakin da Isra'ila ke yi a yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya ya kashe mutan...

Wasu matasa masu baiwar zane-zane sun zayyana yanayin kuncin da faladinawa suke ciki a kan titunan Nairobi babban birnin kasar Kenya domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza. Yakin da Isra'ila ke yi a yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya ya kashe mutane akalla 31,341 tare da jikkata 73,134. Harin bama-bamai da take kaiwa a halin yanzu ya shiga wata na biyar. Wasu gungun matasa ƴan Kenya su ke nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a gaban zanen bango. Hoto: AA Hotunan Murals, a cewar masu zane-zanen waɗanda suka yi zanen, sun bayyana irin tsayin dakar Falasdinawa suka yi a mamayar Isra'ila. Kazalika, wata alama ce da ta nuna adawa da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza. Zane-zanen masu launin daban-daban suna nan da dama a birnin Nairobi wanda suka yi nuni da kayatattun fasahar al'adu akan hanyoyi. Hoto: AA Fasahar al'adu na zane-zanen sun kayatar da hanyoyi sannan suna da matukar tasiri a babban birnin kasar Kenya. Zane-zanen masu launin daban-daban a kan gine-gine da gadoji da kuma unguwannin birnin sun dau hankali sosai. Hotunan zane-zanen na Mural din wata alama ce ta nuna goyon baya da hadin kai ga Falasdinawa da ake ganin suna fuskanatar kisan kiyashi daga sojojin Isra'ila. Hoto: AA Masu zane-zane suna bayyana manufarsu kan al'amuran da suka shafe su ta zamantakewa da siyasa na cikin gida ko kuma a duniya ta hanyar rubuce-rubuce da zane-zane a cikin sauran nau'o'in fasahar kan hanyoyi ko tituna. Artists and activists in Cape Town, South Africa, are showing support for Palestinians in a special way in the historic area of Bo Kaap. They are doing colourful murals demanding an end to Israeli atrocities in Gaza pic.twitter.com/gUL9l0Htei — TRT Afrika (@trtafrika) December 2, 2023