Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Mun gano masu son ta da hargitsi a Kano, za mu bi su har gida mu zaƙulo su – ‘Yan sanda

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano wanda ya yi jawabi a wajen wani taron manema labarai a Kano a daren Litinin ya ce masu son ta da hargitsin sun shirya kai farmaki wasu zaɓaɓɓun wurare a jihar, ciki har da Majalisar Dokokin Jihar. Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce jami'an tsaro a jihar sun g...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:18
Mun gano masu son ta da hargitsi a Kano, za mu bi su har gida mu zaƙulo su – ‘Yan sanda
De un vistazo

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano wanda ya yi jawabi a wajen wani taron manema labarai a Kano a daren Litinin ya ce masu son ta da hargitsin sun shirya kai farmaki wasu zaɓaɓɓun wurare a jihar, ciki har da Majalisar Dokokin Jihar. Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce jami'an tsaro a jihar sun g...

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano wanda ya yi jawabi a wajen wani taron manema labarai a Kano a daren Litinin ya ce masu son ta da hargitsin sun shirya kai farmaki wasu zaɓaɓɓun wurare a jihar, ciki har da Majalisar Dokokin Jihar. Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce jami'an tsaro a jihar sun gano wasu mutane a jihar dake shirin tayar da hargitsi a jihar tare da kai hari wasu muhimman wurare ciki har da Majalisar Dokokin jihar. Kwamishinan 'yan sanda jihar Muhammad Husaini Gumel ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai bayan wata ganawa kan al'amuran tsaro a Gidan Gwamnatin Kano a daren Litinin. Ya ce sun samu wasu bayanai na tsaro, dangane da wasu gungun mutane "da ake ɗaukar su maƙiyan jihar, 'yan daba waɗanda suke ƙoƙarin ƙaddamar da ta'addanci a jihar ta hanyar kai hare-hare a wasu zaɓaɓɓun wurare, musamman Majalisar Dokokin jihar da wasu fitattaun wurare a babban birnin jihar. Ya ce sun samu labari a cikin daren da ya gabata cewa, wasu "suna so su fara ƙona taya su ta da hankalin mutane yadda za a sauya wa Kano suna, ace akwai hargitsi, akwai tashin hankali." Kwamishin ya ƙara da cewa duk wanda yake so ya gwada ƙwanjinsa, to hukumomin tsaro suna da ƙarfin da za su iya rufe ido su koyawa waɗannan maƙiyan na jihar hankali. "Don haka a daren nan ina sanar muku cewa mun yi kyakkyawan shiri wajen fara wani sintiri na gaske tare da gano - musamman - wuraren da muka samu ingantattun bayanan sirri cewa, waɗannan maƙiyan jihar suna ɓuya," a cewar Kwamishinan 'yan sandan Muhammad Gumel. Ya ƙara da cewa duk inda mutanen suka shiga sai sun zaƙulo su. Ya bayyana cewa duk wanda yake so ya yi amfani da saɓanin da aka samu tsakanin masarauta da gwamnati ya ce zai yi amfani da damar domin ta-da-zaune-tsaye to ba za a ƙyale shi ba, ba za a bar shi ba, za a zaƙulo shi, da wanda ya tsaya masa a gurfanar da su gaban shari'a. "Za mu fara bincike gida-gida don kamo duk wani mutum da yake ganin ya fi ƙarfin dokokin jihar," a cewar kwamishinan. Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa an jibge jami'an tsaro a duka fadojin masarautu da kuma Majalisar Dokokin jihar. Ya ƙara da cewa, Kano za ta ci gaba da zama cikin lumana, kuma babu wanda ya isa ya kawo matsala ga zaman lafiyar da ake da shi a jihar. A ranar Lahadi ne wasu mutane suka gudanar da zanga-zanga a kusa da gidan sarki na Nasarawa har ma suka ƙona taya, yayin da suke kira a mayar da Alhaji Aminu Ado Bayero sarautar Kano. To sai dai kwamishinan 'yan sandan ya ce wasu 'ɓata gari' ne suka so su yi amfani da sunan masu goyon bayan Aminu Ado Bayero wajen ta da hargitsin, amma ya ce duka-duka ba su wuce minti goma ba suka watse, "tun ma kafin 'yan sanda su je wajen," kamar yadda ya bayyana. An kuma samu rahotannin makamanciyar wannan zanga-zangar a masaratun Gaya da Bichi. Tun ranar Asabar ne dai aka shiga zaman ɗar-ɗar a Kano bayan komawar Alhaji Aminu Ado Bayero birnin, kwana ɗaya bayan Gwamna Abba Kabir ya sanar da sauke duka sarakunan jihar biyar, ya kuma naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano. "Batun harkar masarauta harumi ne na ɓangaren zartarwa. Wajen da za ka warware duk wata rashin amincewa shi ne kotu," kamar yadda kwamishinan ya bayyana. "Gobe Litinin, an san Kano da kasuwanci, za a buɗe makarantu, za a buɗe bankuna, za a buɗe kasuwanni. Muna da isassun jami'ai da za su yi sintiri a birnin, kada jama'a su ji tsoron komai."