Mai Shari’a Dehinde Dipeolu ce ta yanke hukuncin tare da ba ta damar biyan tarar naira miliyan 100 kan zarge-zarge biyu da hukumar NDLEA ta yi mata waɗanda aka kama ta da laifi a kansu. Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a Legas ta yanke hukuncin ɗaurin shekara 11 ga wata ƴar ƙasar Canada bisa samunta da laifin shigar da wiwi ƙasar. An kama Adrienne Munju mai shekara 41 da kilo 35.20 na wiwi a lokacin da ta shigar da ita Nijeriya. Mai Shari’a Dehinde Dipeolu ce ta yanke hukuncin tare da ba ta damar biyan tarar naira miliyan 100 kan zarge-zarge biyu da hukumar NDLEA ta yi mata waɗanda aka kama ta da laifi a kansu. Mai Shari’ar ta kama Munju da laifin bayan ta amsa laifinta kan zarge-zarge biyun da aka yi mata. Hukumar ta NDLEA ta kama Munju a ranar 3 ga watan Oktobar 2024 a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Ikeja, Legas. Bayan an kama ta, ta shaida wa jami’an NDLEA cewa ta samu aikin safarar wiwin ne ta wani shafin intanet inda aka yi mata tayin dala dubu goma, inda ta ce za ta yi amfani da kuɗin domin biyan kuɗin makarantarta a ƙasar Canada. Ana yawan samun rahotannin safarar miyagun ƙwayoyi a Nijeriya inda akasarinsu ake shigar da su ƙasar daga wasu ƙasashen waje. Sai dai hukumar ta NDLEA ta sha jaddada cewa tana iya bakin ƙoƙarinta domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyin. Ko a kwanakin baya sai dai hukumar ta ce ta kama ƙwayar tapentadol guda miliyan 25 wanda kuɗinta ya haura naira biliyan 13 sai kuma kwalaben kodin 350,000 waɗanda kuɗinsu ya haura naira biliyan biyu.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Miyagun ƙwayoyi: Kotun Nijeriya ta yanke wa 'yar Canada hukuncin shekara 11 a gidan yari
Mai Shari’a Dehinde Dipeolu ce ta yanke hukuncin tare da ba ta damar biyan tarar naira miliyan 100 kan zarge-zarge biyu da hukumar NDLEA ta yi mata waɗanda aka kama ta da laifi a kansu. Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a Legas ta yanke hukuncin ɗaurin shekara 11 ga wata ƴar ƙasar Canada bisa samunt...

Mai Shari’a Dehinde Dipeolu ce ta yanke hukuncin tare da ba ta damar biyan tarar naira miliyan 100 kan zarge-zarge biyu da hukumar NDLEA ta yi mata waɗanda aka kama ta da laifi a kansu. Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a Legas ta yanke hukuncin ɗaurin shekara 11 ga wata ƴar ƙasar Canada bisa samunt...
