Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Masar Ta Yi Kira ga Isra’ila Ta Fice daga Gaza

An nemi sake buɗe mashigar Rafah a matsayin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, ya yi kira ga Isra’ila da ta fice daga Gaza tare da sake buɗe mashigar Rafah, a matsayin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a bara. Ya bayyana hakan ne...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:17
Masar Ta Yi Kira ga Isra’ila Ta Fice daga Gaza
Bu haberde ne var?

An nemi sake buɗe mashigar Rafah a matsayin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, ya yi kira ga Isra’ila da ta fice daga Gaza tare da sake buɗe mashigar Rafah, a matsayin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a bara. Ya bayyana hakan ne...

An nemi sake buɗe mashigar Rafah a matsayin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, ya yi kira ga Isra’ila da ta fice daga Gaza tare da sake buɗe mashigar Rafah, a matsayin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a bara. Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, a birnin Alkahira. (TRT Hausa) A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar, tattaunawar ta mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar dabarun tsaro tsakanin Masar da Amurka, da kuma bunƙasa alaƙar siyasa da tattalin arziki, tare da duba halin da ake ciki a Gaza, Sudan, yankin Kahon Afirka da kuma tsaron ruwa na Masar. (TRT Hausa) Abdelatty ya maraba da shigar Masar cikin abin da ya kira “Kwamitin Zaman Lafiya” na Shugaban Amurka Donald Trump, yana mai jaddada muhimmancin aiwatar da mataki na biyu na shirin Trump kan Gaza, tare da goyon bayan kwamitin ƙasa da aka ɗora wa alhakin kula da yankin. (TRT Hausa) Ya kuma nemi a gaggauta tura dakarun ƙasa da ƙasa domin sa ido kan tsagaita wuta, da sake buɗe mashigar Rafah daga ɓangarorin Gaza da Masar, tare da tabbatar da ficewar Isra’ila daga Gaza domin share fagen farfaɗowa da sake gina yankin. (TRT Hausa) A wani ɓangare, rahotanni daga Isra’ila sun ce Washington ta cimma matsaya da Firaminista Benjamin Netanyahu kan sake buɗe mashigar Rafah, inda kafar yaɗa labarai ta Walla ta ce ana sa ran buɗe mashigar nan da ƙarshen makon nan. (TRT Hausa) Yarjejeniyar tsagaita wuta ta dakatar da yaƙin Isra’ila a Gaza wanda ya ɗauki kusan shekaru biyu, inda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 71,000 — yawancinsu mata da yara — tare da jikkata sama da 171,000 tun watan Oktoban 2023. (TRT Hausa)