Isra'ila na aikata 'munanan' laifuka a Gaza, kuma dole shirun da wasu kasashe suka yi ya zo karshe, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi kira ga dukkan kasashen Kugiyar Hadin Kan Kasashen Yankin Gulf' (GCC) da su yi duk mai yiwuwa wajen matsa lamba ga Isra'ila da ƙawayenta. Da yake bayani a wajen taron Tattaunawa Dabaru na Ministocin harkokin Wajen Turkiyya da Kasashen Yankin Gulf a ranar Lahadi a DOha, babban birnin Qatar, Fidan ya ce "Ba za a yi biris da mummunan halin da fursunoni Falasdinawa ke ciki ba." Ya ce "Mu daure mu rufe idanu mu kare dokokin kasa da kasa, kare hakkokin ɗan'adam da darajojin duniya, wadanda wasu abokanmu na Yammacin Duniya suka manta." "Hadin kai a tsakaninmu zai zama mai muhimmanci wajen dabbaka zaman lafiya da samar a tsaro a yankin, sai mu fara da samar da mafita ga 'yan uwanmu Falasdinawa," in ji Ministan na Harkokin Wajen Turkiyya. Fidan ya jaddada cewa Isra'ila na aikata 'munanan' laifuka a Gaza, kuma dole shirun da wasu kasashe suka yi ya zo karshe. "A shirye muke mu bayar da gudunmawa wajen sake gina Gaza, amma wadanda suka rusa Gaza ta taimaka wa wajen rusa yankin, ya zama wajibi su biya wannan barna da suka yi," in ji shi. Hakan Fidan ya bayyana cewa tirjiya ga mamayar Falasdin ya zama gwagwarmaya tsakanin wadand aqke zalunta da azzalumai a duniya baki daya Ya ce "Amincewa da 'yantacciyar kasar Falasdinu da kasashe da dama ke ci gaba da yi d akuma zaman ta cikakkiyar mambar MDD, na daga dokokin ƙasa da ƙasa, adalci da tunani mai kyau na Majalisar Dinkin Duniya." "A matsayinmu na Turkiyya, za mu ci gaba da yin dukkan kokari wajen ganin an kafa ƙkasar Falasdinu 'yantacciya, mai cikakken ikon mulki da kan iyakoki," in ji Fidan. Ƙawance da Ƙasashen Yankin Gulf Fidan ya bayyana imaninsa kan cewar taron zai haifar da ɗa mai ido, yana mai cewa "A matsayinmu na Turkiyya, muna bayar da muhimmanci sosai ga alakrmu da kasashen Gulf." "Matakin da muka kai yau a lakarmu ya smau ne saboda kokarin da kowanne bangare ke yi, kuma kow ana gamsuwa. Alakarmu na ci gaba da habaka a kowanne bangare." Fidan ya kuma ce jarin kasuwanci tsakanin Turkiyya da kasashen Gulf ya karu da kusan kasho 40 a 2023 idan akwa kwatanta da shekarar 2022, wand aya kai dala biliyan $31.4. kuma a shekaru 20 da suka shude jarin kasuwancin ya ninka sau 16. Ya yi karin haske da cewa Turkiyya na daya daga mayna wuraren yawon bude ido ga kasashen Gulf, yana mai tsokaci da cewa sama da jama'ar yankin Gulf miliyan 1.3 ne suka ziyarci Tukiyya a 2023. Isra'ila na ci gaba da kai munanan hare Gaza tun 7 ga Oktoba bayan da kungiyar tirjiya ta Hamas ta kai musu harin kan iyaka, duk matakin da MDD ta dauka amma Isra'ila ba ta dakata ba. Sama da Falasdinawa 37,000 ne suka mutu a Gaza, mafi yawan su mata da yara kanana, ind akusan 84,500 suka jikkata, kamar yadda hukumomin lafiya na yankin suka sanar. Watanni takwas kenan da fara yakin isra'ila a Gaza, inda kawanye da rufe hanoyoyin yankin ya jefa jama'a cikin wahalar abinci da tsaftatacen ruwan sha da magunguna. Ana zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi a kotun Kasa da Kasa Mai Hukunta Manyan Laifuka, wadda hukuncinta na baya-bayan nan ya umarci Tel Aviv d ata gaggauta dakatar da hare-hare kan kudancin Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan guda suke neman mafaka bayan an afka wa yankin a ranar 6 ga Mayu.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya buƙaci kasashen GCC da su matsa wa Isra'ila da ƙawayenta lamba
Isra'ila na aikata 'munanan' laifuka a Gaza, kuma dole shirun da wasu kasashe suka yi ya zo karshe, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi kira ga dukkan kasashen Kugiyar Hadin Kan Kasashen Yankin Gulf' (GCC) da su yi duk mai yiwuwa wajen...

Isra'ila na aikata 'munanan' laifuka a Gaza, kuma dole shirun da wasu kasashe suka yi ya zo karshe, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi kira ga dukkan kasashen Kugiyar Hadin Kan Kasashen Yankin Gulf' (GCC) da su yi duk mai yiwuwa wajen...
