“Gaza a baya ta kasance gidan yarin da ke a buɗe. Sai dai a halin yanzu ta kasance fagen daga wanda Firaiministan Isra’ila (Benjamin Netanyahu) yake gudanar da ayyukan kashe farar hula domin rayuwarsa ta siyasa,” in ji Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya caccaki kasashen waje kan gazawa wurin dakatar da yakin da Isra’ila ke yi a kan Falasdinawa a Gaza, inda ya bayyana fargabar bazuwar yaƙin zuwa sassan yankin. “Kwanaki ɗari da tara da fara yaƙi, abin kunya ne kan cewa kasashen duniya sun kasa dakatar da zubar da jini a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan,” kamar yadda Fidan ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya kan halin da Gabas ta Tsakiya take ciki, daga ciki har da Falasdinu wadda ake magana a kanta, a ranar Talata. “Zancen da ake yi kan cewa wannan yaƙin ana yinsa ne domin bai wa Isra’ila kariya ba abin gamsarwa bane. Sai dai ginshikan waɗannan zantunttuka da ake yi ba su taɓo batun tsaron Falasɗinawa ko kuma yadda Falasɗinawan za su kare kansu,” kamar yadda ya kara da cewa. Taron wanda aka yi ƙarƙshin Antoni Gutteres wanda shi ne Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya samu halartar manyan ministocin harkokin wajen kasashe da kuma jakadu daga ƙasashe biyar mambobin kwamitin da kuma wasu kasashe. Hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Gaza sun jawo matuƙar buƙatar ayyukan jin kai inda adadin mutanen da ake kashewa ke karuwa a kullum. “Gaza a baya ta kasance gidan yarin da ke a buɗe. Sai dai a halin yanzu ta kasance fagen daga wanda Firaiministan Isra’ila (Benjamin Netanyahu) yake gudanar da ayyukan kashe farar hula domin rayuwarsa ta siyasa,” in ji Fidan. Kisan kiyashi Da yake jaddada cewa Isra'ila na aikata manyan laifuffukan yaki, Fidan ya bayyana damuwarsa kan cewa wadannan laifuffukan sun kai na kisan kiyashi, ya kuma ce dole ne a hukunta wadanda ke da hannu domin dawo darajar dokokin kasa da kasa a idon duniya. Ministan harkokin wajen kasar ya kuma jaddada bukatar kauce wa kara bazuwar wannan rikicin a yankin, inda ya kara nanata gargadin da Turkiyya ta yi ta yi kan hadarin da ke tattare da bazuwar rikicin. Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a cikin tekun Bahar Maliya, Yemen, Lebanon, Iraki, Siriya, Iran da Pakistan na da matukar tayar da hankali. Wannan rikicin zai iya zama kamar wata ambaliya wadda za ta iya haɗiye kowa da kowa kuma babu wanda zai tsira cikin sauƙi,” kamar yadda ya yi gargaɗi.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan ya caccaki kasashen duniya kan gazawa wajen dakile zubar da jini a Gaza
“Gaza a baya ta kasance gidan yarin da ke a buɗe. Sai dai a halin yanzu ta kasance fagen daga wanda Firaiministan Isra’ila (Benjamin Netanyahu) yake gudanar da ayyukan kashe farar hula domin rayuwarsa ta siyasa,” in ji Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya caccaki kasashen waje k...

“Gaza a baya ta kasance gidan yarin da ke a buɗe. Sai dai a halin yanzu ta kasance fagen daga wanda Firaiministan Isra’ila (Benjamin Netanyahu) yake gudanar da ayyukan kashe farar hula domin rayuwarsa ta siyasa,” in ji Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya caccaki kasashen waje k...
