Ganawar za ta mayar da hankali kan tsaro, cinikayya da batutuwan Gaza da Somalia Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai gana da takwaransa na Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, wanda zai kai ziyara Ankara ranar Litinin, inda ake sa ran tattauna rawar da Nijeriya ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a Yammacin Afirka da kuma hanyoyin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. (TRT Hausa) A yayin ganawar, ana sa ran Fidan zai jaddada muhimmancin kyautata cinikayya da zuba jari tsakanin Turkiyya da Nijeriya, tare da tattauna buƙatun kamfanonin Turkiyya da ke gudanar da kasuwanci a Nijeriya, da kuma faɗaɗa haɗin kai a fannonin soji da tsaro domin yaƙi da ta’addanci. (TRT Hausa) Haka kuma tattaunawar za ta shafi batutuwan Gaza da Somalia, inda Fidan zai nemi haɗin kai tsakanin Ankara da Abuja a cikin ƙungiyoyin duniya kamar Majalisar Ɗinkin Duniya, OIC da D-8, tare da tabbatar da dorewar tsagaita wuta a Gaza da kyautata yanayin jinƙai. (TRT Hausa) Ministan zai kuma jaddada buƙatar kare ‘yancin kan Somalia, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Nijeriya wajen mutunta dokokin ƙasa da ƙasa, a cewarsu. (TRT Hausa) A ɓangaren tattalin arziki, cinikayya tsakanin ƙasashen biyu ta kai dala miliyan 688.4 a watanni 11 na shekarar 2025, inda Nijeriya ta zama babbar ƙawar kasuwancin Turkiyya a yankin Sahara, tare da kamfanonin Turkiyya fiye da 50 da ke gudanar da kasuwanci a Nijeriya. (TRT Hausa)
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Zai Gana da Takwaransa na Nijeriya a Ankara
Ganawar za ta mayar da hankali kan tsaro, cinikayya da batutuwan Gaza da Somalia Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai gana da takwaransa na Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, wanda zai kai ziyara Ankara ranar Litinin, inda ake sa ran tattauna rawar da Nijeriya ke takawa wajen wanzar d...

Bu haberde ne var?
Ganawar za ta mayar da hankali kan tsaro, cinikayya da batutuwan Gaza da Somalia Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai gana da takwaransa na Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, wanda zai kai ziyara Ankara ranar Litinin, inda ake sa ran tattauna rawar da Nijeriya ke takawa wajen wanzar d...
