Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da Sakatare Janar na MDD Guterres sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya sun tattauna kan kan halin da ake ciki a yankin Gaza, a cewar majliyoyin diplomisiyyar Turkiyya. Ministan Harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da Sakatare Janar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:17
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da Sakatare Janar na MDD Guterres sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya
Bu haberde ne var?

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya sun tattauna kan kan halin da ake ciki a yankin Gaza, a cewar majliyoyin diplomisiyyar Turkiyya. Ministan Harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da Sakatare Janar...

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya sun tattauna kan kan halin da ake ciki a yankin Gaza, a cewar majliyoyin diplomisiyyar Turkiyya. Ministan Harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antoniyo Guterres, a cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiya. A wata tattaunawa ta waya ranar Litinin, Fidan da Guterres sun yi kuma tattauna kan halin da ake ciki a Gaza. Batun Cyprus da safarar teku cikin aminci a Bahrul Aswad na daga cikin batutuwan da aka tattauna, a cewar majiyar. Tehran ta kai hare-hare sama da 300 da makamai masu linzami da jirage marasa matuka a fadin kasar Isra'ila a yammacin ranar Asabar a matsayin ramuwar gayya kan harin da jiragen Tel Aviv suka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus babban birnin kasar Syria, a ranar 1 ga Afrilu inda dakarun kare juyin juya halin Musulunci bakwai, ciki har da janar-janar guda biyu suka mutu. Dangane da abubuwan da suka faru a yankin gabas ta tsakiya,Turkiyya ta ce za ta ci gaba da kokarin hana afkuwar wani tsari da zai lalata zaman lafiyar yankin har abada da kuma haifar da rigingimu a duniya. Ankara ta ce "tana sake aikewa da sakwanni karara ga mahukuntan Iran da kuma kasashen yammacin duniya da ke da tasiri a kan Isra'ila, don yin kira ga kowa da kowa da ya kawo karshen tashin hankalin".