Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Amurka da kai hari duk da tattaunawa da ake yi Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa Iran ba ta ganin yiwuwar sake shiga tattaunawa da Amurka bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyar ƙasar. A wata hira da kafar watsa labarai ta PBS News, Araghchi ya ce zai yi wuri a yi tsokaci kan ko sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, zai buɗe ƙofar sabuwar tattaunawa ko tsagaita wuta da Amurka. Sai dai ya jaddada cewa bayan abin da ya kira mummunan hari da Amurka ta kai, batun sake tattaunawa ko cimma yarjejeniya da Amurka ba ya cikin ajandar Iran a yanzu. Ya yi ishara da yaƙin kwanaki 12 da ya faru a watan Yuni, lokacin da Isra’ila da dakarun Amurka suka kai hari kan tashoshin nukiliyar Iran duk da cewa ana tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. Araghchi ya ce a baya tattaunawar da aka yi a Geneva ƙarshen watan Fabrairu ta nuna alamun samun ci gaba, amma duk da haka Amurka ta ci gaba da kai hare-hare. Game da rikicin yankin, ministan ya ce Iran ba ita ce ta janyo tsaikon da ake samu a kasuwancin man fetur na duniya ba. Ya ce hare-haren Amurka da Isra’ila ne suka sa yankin ya zama mai rashin tsaro, lamarin da ya sa jiragen ruwa da tankokin mai ke tsoron wucewa ta mashigin ruwan Hormuz. Araghchi ya kuma yi watsi da zarge-zargen cewa Iran na kai hare-hare kan jiragen ruwa domin katse jigilar mai, yana mai cewa matakan da Iran ke ɗauka kariya ce ta halal. Ya kuma gargaɗi cewa idan Amurka ta kai hari kai tsaye kan Iran, Tehran za ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan sansanonin sojin Amurka da kadarorinta a faɗin yankin. Tushen labari: Newstimehub
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Iran ta yi watsi da yiwuwar sake tattaunawa da Amurka
Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Amurka da kai hari duk da tattaunawa da ake yi Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa Iran ba ta ganin yiwuwar sake shiga tattaunawa da Amurka bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyar ƙasar. A wata hira da...

Em resumo
Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Amurka da kai hari duk da tattaunawa da ake yi Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa Iran ba ta ganin yiwuwar sake shiga tattaunawa da Amurka bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyar ƙasar. A wata hira da...
