الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Mele Kyari: EFCC ta yi wa tsohon shugaban NNPCL tambayoyi

EFCC tana bincike ne kan yadda aka kashe kimanin dala biliyan biyu a gyaran matatun mai na Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari. Tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ranar Laraba ya je hedkwatar h ukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar ta’annati (EFCC)...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:17 ص
Mele Kyari: EFCC ta yi wa tsohon shugaban NNPCL tambayoyi
لمحة سريعة

EFCC tana bincike ne kan yadda aka kashe kimanin dala biliyan biyu a gyaran matatun mai na Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari. Tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ranar Laraba ya je hedkwatar h ukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar ta’annati (EFCC)...

EFCC tana bincike ne kan yadda aka kashe kimanin dala biliyan biyu a gyaran matatun mai na Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari. Tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ranar Laraba ya je hedkwatar h ukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar ta’annati (EFCC) domin amsa tambayoyi kan yadda ya tafiyar da harkokin kuɗi a lokacin da yake shugabanci a kamfanin . Bayanai sun nuna cewa Kyari ya isa hedkwatar EFCC a Abuja da misalin ƙarfe 2:15 na ranar Laraba. Rahotanni daga kafofin watsa labaran Nijeriya sun ce EFCC tana bincike ne kan yadda aka kashe kimanin dala biliyan biyu a gyaran matatun mai na ƙasar a ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari, waɗanda suka haɗa da dala biliyan 1.55 da aka kashe a kan Matatar Mai ta Fatakwal, da dala miliyan 740.6 a Matatar Kaduna da kuma dala miliyan 656.9 a Matatar Warri. Yayin da ya isa hedkwatar EFCC, an ambato tsohon shugaban na NNPCL yana cewa, “Na yi nawa [aikin]; dole EFCC su yi nasu. Idan ko wannenmu ya yi nasa aikin—ba tare da tsoro ko alfarma ba, cikin gaskiya, da girmamawa da jajircewa—Nijeriya za ta ci gaba.” Sai dai daga bisani bayanai sun tabbatar da cewa Mele Kyari ya bar hedkwatar hukumar ta EFCC. A watan jiya ne wata babbar kotun Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ke Abuja ta ba da umarnin hana amfani na wucin-gadi da asusun banki huɗu da ke da alaƙa da tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya, NNPCL, Mele Kyari bisa zarge-zargen almundahana.