Sojojin Isra'ila na saka kayan matan da suka kashe a gidajensu, wasu na fasa ɗakunan girki suna sata a gidajen da aka gudu aka bari, wasu na hawa kekunan yaran Gaza da aka raba da gidajensu. Ana ta tambaya kan halayyar sojojin Isra'ila a Gaza. Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na yawan yabon sojojinsa da cewa su ne mafiya tarbiyya a duniya, tun bayan da a watan Oktoban bara ya aika su zuwa Gaza don kai hare-hare. Sai dai kuma, hotunan da ake yaɗa wa a shafukan sada zumunta na intanet irin su TikTok da Telegram da X na nuna yadda sojojin Isra'ila ke nuna munanan ɗabi'u, waɗanda ba su yi kama da na nuna ƙwarewar soji ba. A wasu daga cikin waɗannan bidiyoyin, an ga sojojin Isra'ila na saka kayan mata da fasa ɗakunan girki suna sace kayayyakin da aka bari, sannan suna hawa kekunan yara ƙanana a Gaza, a yayin da suka lalata gidajensu. Wani ɓangare mai yawa na bidiyon da aka yaɗa ya nuna sojoji suke cinna wa bututu wuta, kuma aka ga yadda gidaje ke ƙonewa, suna lalata kayan gwamnati da na makarantu, da kuma zagi da cin mutuncin Falasɗinawa. "Wasu daga ɗabi'un rashin tarbiyyar da sojojin Isra'ila suka nuna a bidiyon za su ɓata wa mutane da yawa rai, kuma su kunyata ƙwararrun sojoji da suka fahimci aiki da ladabi, kuma suka san me ake nufi da ladabi da hali mai kyau ga jami'in soji," in ji John D. Alternburg, Manjo Janar mai ritaya a rundunar sojin Amurka yayin tattaunawa da TRT Afrika. Tsohon jami'in sojin na Amurka ya ce wasu daga waɗannan bidiyoyi za su sanya a dinga yi wa dakarun sojin isra'ila kallo mara kyau "a cikin gida da ƙetare". A yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare ba ƙaƙƙautawa a Zirin Gaza da aka mamaye, ya zuwa yanzu ta kashe aƙalla Falasɗinawa 31,000 da jikkata sama da 71,000, an ga yadda sojojin Isra'ila ke rushe gine-gine da isgilanci ga Falasɗinawa. Bidiyoyin da sojojin Isra'ila suka dinga yaɗawa da kansu sun nuna yadda suke yin abubuwa da yawa tun daga ayyukan soji zuwa lalata kayayyakin jama'a. A watan jiya, babban lauyan sojojin Manjo Janar Yifat Tomer-Yerushalm ya yi gargaɗi na ba-zata a wata wasiƙa ga dakarun da suka yi kutse kan su guji "aikata muggan laifuka" "Akwai buƙatar a mayar da hankali sosai ga illar da nuna hali mara kyau zai iya raga ƙimar rundunar sojin," in ji Anltenburg. Duk da rahotannin da aka samu na gargaɗin da manyan soji ke yi wa ƙananan, sojojin Isra'ila a Gaza na ci gaba da lalata kayayyaki tare da cin fuska Falasɗinawa. Misali, a wani bidiyo an ga sojoji a kan kekuna. A wani kuma, an ga soja ya ɗauki darduman Sallah ya jefa su banɗaki. A wani bidiyon kuma, an ga soja na ɗaukar bidiyon kamfen mata da aka bari a gidajen. A wani bidiyon da bai fita sosai ba ma, an ga soja na ƙoƙarin cinna wuta kan kayan abinci don jefa Falasɗinawa cikin yunwa. A yayin da a baya ma an samu lokutan da sojojin isra'ila suka nuna rashin tarbiyya, yakin da suke yi a Gaza na zuwa ne a zamanin da ake da cigaban sadarwa. Kasancewar sojoji na dauke da manyan wayoyin hannu, manyan na'urorin sadarwa, tazarar da ke tsakanin sadarwar zamani da filin daga ta kau. Wannan ta'ada na sanya yaduwar hotuna d abidiyon da ba a tantance su ba - wadanda ka iya sauya tunanin jama'a game d ayakin da ake yi. Wannan na kuma kawo tsanantar munanar da yakin ya yi har zuwa dakunanmu. Bayyanar waɗannan bidiyoyi ya janyo tambayoyi game da halayyar sojojin Isra'ila a Gaza da kuma batun dokokin ƙasa da ƙasa da kare haƙƙokin ɗan'adam. Abubuwa masu tsoratarwa "A yayin da a baya ma akwai irin yaɗa waɗannan bidiyoyi ykamar a rikicin Rasha da Ukraine, da ma a yayin da Amurka ta kutsa kai Iraki da Afganistan, amma waɗannan bidiyoyin na Isra'ila sun fita daban saboda yadda suke da muni da nuna halin ko in kula ga rayuwar Falasɗinawa fararen-hula," in ji Waleed F, Mahdi, Mataimakin Farfesa a Jami'ar Oklahoma yayin tattaunawa ta TRT World. Mahdi ya kuma ce ba a yi mamaki ba yadda sojojin Isra'ila ke yaɗa hotuna da bidiyon don jan hankali, wanda mafi yawancin lokuta hakan ya saba wa dokokin rundunar sojin Isra'ila. Kwararren ya ce "Tabbas akwai wani mataki na nuna an fi karfin doka wand ake sanya wadannan sojoji nuna rashin tarbiyya. Akwai kuma wani dalili na tunani kan yaki da ke fayyace wadannan aika-aika." Salo da tsari Tasirin wadannan bidiyo ya wuce na tsakanin bakunan da kwakwalen jama'a kawai, ana tsammanin daukar mataka shari'a a nan gaba. An samu bidiyo da dama da suka zama shaidar an yi kisan kiyashi da za a iya amfani da su a gaban kotu, ciki har wadanda Afirka ta Kudu ta gabatar a gaban Kotun Kasa da Kasa Mai Hukunta Manyan Laifuka, tana zargin Isra'ila d aaikata kisan kiyashi. Farfesa Lisa Hajjar, wadda ta yi shuhura d abincikenta a Sashen Nazarin Zamantakewar Dan Adam a Jami'ar California, Santa Barbara, ta yi zurfi kan dokokin zamantakewa, yaki, 'yancin ɗan'adam da rikicin siyasa da al'amuran kasa da kasa a yau. A tattaunawar da ta yi da TRT World, ta yi karin haske kan muhimmancin yadda sojojin Isra'ila ke ajje bayanan ta'annatin da suke yi. Ta ce "Wannan abu da Isra'ila ke yi wani salo da tsari ne da ke cikin ayyukan gwamnatin Isra'ila inda a koyaushe ake zagin Falasɗinawa da wulaƙanta su. Wannan halayya, da ake murna yayin yin ta na sake tabbatar da tsana da ƙiyayya ga Falasdinawa wanda ya saba wa mutunta ɗan'adam." Daɗin daɗawa, game da batutuwan doka da shari'a kan waɗannan bidiyoyi, bayyana ya sake bankaɗo da irin rawar da shafukan sadarwa na intnet ke takawa wajen sauya ra'ayin mutane game da yaƙin da ake yi. A yayin da dukkan duniya ta yi amo wajen mayar da martani kan waɗannan bidiyoyi da hotuna, ana sake kiran da a yi gaskiya, ana buƙatar da a ɗauki matakan magance wannan ta'annati. Mahdi daga Oklahoma ya ce "Rashin tabbacin ko Isra'ila na ɗaukar matakan ladabtarwa kan waɗannan sojoji ko ba ta ɗauka, na buɗe ƙofar zato kan ko ayyukan na ɗaiɗaikun mutane ne ko kuma tsara su aka yi a hukumance."
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Me ya sa sojojin da ke iƙirarin sun fi na ko ina tarbiyya a duniya ke yin aika-aika a Gaza?
Sojojin Isra'ila na saka kayan matan da suka kashe a gidajensu, wasu na fasa ɗakunan girki suna sata a gidajen da aka gudu aka bari, wasu na hawa kekunan yaran Gaza da aka raba da gidajensu. Ana ta tambaya kan halayyar sojojin Isra'ila a Gaza. Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na yawan ya...

Em resumo
Sojojin Isra'ila na saka kayan matan da suka kashe a gidajensu, wasu na fasa ɗakunan girki suna sata a gidajen da aka gudu aka bari, wasu na hawa kekunan yaran Gaza da aka raba da gidajensu. Ana ta tambaya kan halayyar sojojin Isra'ila a Gaza. Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na yawan ya...
