Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

MDD na gazawa wajen shawo kan ƙalubalen da duniya ke fuskanta: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya

"Ana buƙatar babban sauyi da gyara a Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman a Kwamitin Tsaro," in ji Hakan Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki Majalisar Ɗinkin Duniya kan gazawarta wajen nuna ingantaccen jagoranci da zai shawo kan ƙalubalen da duniya ke fuskanta a yau. "Ƙasashe...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:17
MDD na gazawa wajen shawo kan ƙalubalen da duniya ke fuskanta: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya
Кратко

"Ana buƙatar babban sauyi da gyara a Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman a Kwamitin Tsaro," in ji Hakan Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki Majalisar Ɗinkin Duniya kan gazawarta wajen nuna ingantaccen jagoranci da zai shawo kan ƙalubalen da duniya ke fuskanta a yau. "Ƙasashe...

"Ana buƙatar babban sauyi da gyara a Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman a Kwamitin Tsaro," in ji Hakan Fidan. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki Majalisar Ɗinkin Duniya kan gazawarta wajen nuna ingantaccen jagoranci da zai shawo kan ƙalubalen da duniya ke fuskanta a yau. "Ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya na fuskantar jarrabawa a tarihi," Fidan ya faɗa wa Babban Taron MDD kan Makoma a birnin New York a ranar Litinin. "Abin takaici, Majalisar Ɗinkin Duniya ta gaza nuna jogarancin da ya kamace ta na shawo kan barazanar da ke fuskantar ɗan'adam a yau." Babban taron ya tattara shugabanni waje guda da manufar neman amincewar ƙasashe kan yadda za a samu makoma mai kyau. Fidan ya ƙara da cewa ana buƙatar sabon tsari mai tasiri, wanda zai samar da mafita ta bai-ɗaya ga matsalolin duniya. "Ana buƙatar gyaran da zai taɓo ko'ina" "Muna buƙatar tsarin da zai taɓo kowanne ɓangare a ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman a Kwamitin Tsaro," in ji shi. Tun da jimawa Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ke ta ƙoƙarin ganin an kawo sauyi a ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya inda yake amfani da taken "Duniya ta fi ƙasashe biyar girma," inda yake nufi da yadda babu adalci wajen zama mamba a Kwamitin Tsaro na Majalisar. Erdogan ya kuma nuna rashin jin daɗi kan rashin tasirin da MDD ke da shi wajen magance rikice-rikive da dama a duniya, musamman yaƙin Isra'ila a Gaza da ya kusa shekara guda, wanda aka kashe mutane 41,000, mafi yawan su mata da yara, tare da jikkata fiye da mutum 95,000.