Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Mayaƙan Boko Haram sun miƙa wuya ga sojojin Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta ce mayaƙan ƙungiyar ta Boko Haram sun yi saranda ne sakamakon samamen da take kai wa a yankunan da suke a jihar Borno. Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram goma sha biyar sun yi saranda ga sojojin Nijeriya ranar Lahadi, a cewar wata sanara da rundunar sojin ta fitar. Sanarwar ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:17
Mayaƙan Boko Haram sun miƙa wuya ga sojojin Nijeriya
En bref

Rundunar sojin Nijeriya ta ce mayaƙan ƙungiyar ta Boko Haram sun yi saranda ne sakamakon samamen da take kai wa a yankunan da suke a jihar Borno. Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram goma sha biyar sun yi saranda ga sojojin Nijeriya ranar Lahadi, a cewar wata sanara da rundunar sojin ta fitar. Sanarwar ta...

Rundunar sojin Nijeriya ta ce mayaƙan ƙungiyar ta Boko Haram sun yi saranda ne sakamakon samamen da take kai wa a yankunan da suke a jihar Borno. Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram goma sha biyar sun yi saranda ga sojojin Nijeriya ranar Lahadi, a cewar wata sanara da rundunar sojin ta fitar. Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar sojin ta ƙaddamar da wani gagarumin samame a yankin Aguata da ke jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar. Ta ce mayaƙa 15 na ƙungiyar sun yi saranda sakamakon samamen sannan an lalata maɓoyarsu. Boko Haram ta ƙaddamar da kai hare-hare a arewa maso gabashin Nijeriya tun 2009, inda ta kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu. Tun 2015, ƙungiyar ta riƙa kai hare-hare a ƙasashe maƙwabtan Nijeriya irin su Kamari, Chadi da Jamhuriyar Nijar. Sai dai dubban mayaƙan Boko Haram sun miƙa wuya sannan jami'an tsaro sun kashe ɗaruruwa tun bayan da suka ƙara ƙaimi a yaƙin da suke yi da ƙungiyar.