Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Matsalar ƙarancin abinci za ta ta'azzara a Sudan saboda farin ɗango — MDD

Ana fargabar cewa matsalar ƙarancin abinci za ta iya ƙaruwa a Sudan sakamakon irin ɓarnar da farin ɗango suka yi a gonaki da dama a Sudan. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa abinci zai ƙara ƙaranci a watanni masu zuwa a daidai lokacin da Sudan ke shiga watannin ƙarancin abinci. Hukumar S...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:17
Matsalar ƙarancin abinci za ta ta'azzara a Sudan saboda farin ɗango — MDD
Kwa muhtasari

Ana fargabar cewa matsalar ƙarancin abinci za ta iya ƙaruwa a Sudan sakamakon irin ɓarnar da farin ɗango suka yi a gonaki da dama a Sudan. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa abinci zai ƙara ƙaranci a watanni masu zuwa a daidai lokacin da Sudan ke shiga watannin ƙarancin abinci. Hukumar S...

Ana fargabar cewa matsalar ƙarancin abinci za ta iya ƙaruwa a Sudan sakamakon irin ɓarnar da farin ɗango suka yi a gonaki da dama a Sudan. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa abinci zai ƙara ƙaranci a watanni masu zuwa a daidai lokacin da Sudan ke shiga watannin ƙarancin abinci. Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya FAO ta yi gargaɗi a Geneva cewa irin ɓarnar da farin ɗango suka yi wa amfanin gona ya yi matuƙar haddasa matsaloli tun daga tsakiyar shekarar da ta gabata. Mataimakin wakilin FAO a Sudan Adam Yao ya yi gargaɗi kan cewa matsalolin farin ɗangon sun kai wani “mataki na barazana”, kuma ba tare da tsare-tsare masu ɗorewa ba na daƙile bazuwarsu ba, za a ci gaba da tafka asara. Wannan na faruwa ne sakamakon rashin ayyukan sa ido a tsakiya da yammacin Sudan sakamakon yaƙin da ake gwabzawa tsakanin sojojin ƙasar da kuma dakarun RSF. Kiyaye gonaki A wani ɓangaren, jami’an da ke sa ido kan farin ɗango tare da goyon bayan FAO sun yi ƙoƙarin sa ido kan sama da kadada 113,500 da kuma aiki a kan kadada 23,000 wadda farin suka yi wa ɓarna. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana ƙiyasin cewa mutum miliyan 18 suna fama da ƙarancin abinci – wanda hakan ke nufin an samu ƙarin mutum miliyan goma fiye da bara. Hukumomin bayar da agaji sun yi ƙoƙarin kai kayan agaji ga mutum miliyan bakwai a Sudan tun daga Afrilun bara.