Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Matatar mai ta Dangote ta soma sayar da fetur a Nijeriya

Matatar mai ta Dangote da ke Nijeriya ta fara sayar da fetur a ƙasar a ranar Talata, in ji ƙungiyar tallatawa da sayar da mai ta kamfanin. Matatar mai ta Dangote da ke Nijeriya ta fara sayar da fetur a ƙasar a ranar Talata, in ji ƙungiyar tallatawa da sayar da mai ta kamfanin. Wannan babban matak...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:17
Matatar mai ta Dangote ta soma sayar da fetur a Nijeriya
Kwa muhtasari

Matatar mai ta Dangote da ke Nijeriya ta fara sayar da fetur a ƙasar a ranar Talata, in ji ƙungiyar tallatawa da sayar da mai ta kamfanin. Matatar mai ta Dangote da ke Nijeriya ta fara sayar da fetur a ƙasar a ranar Talata, in ji ƙungiyar tallatawa da sayar da mai ta kamfanin. Wannan babban matak...

Matatar mai ta Dangote da ke Nijeriya ta fara sayar da fetur a ƙasar a ranar Talata, in ji ƙungiyar tallatawa da sayar da mai ta kamfanin. Matatar mai ta Dangote da ke Nijeriya ta fara sayar da fetur a ƙasar a ranar Talata, in ji ƙungiyar tallatawa da sayar da mai ta kamfanin. Wannan babban matakin tsayawa da ƙafafu ga Nijeriya wajen biyan buƙatar makamashi da take da ita. Mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka Aliko Dangote ne ya gina matatar man, mafi girma a nahiyar a gaɓar tekun Legas kan dala biliyan 20, kuma an kammala aikin bayan tsaiko na shekaru da dama da aka samu. Matatar na iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 kowace rana, kuma idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta zama mafi girma a Afirka da Turai. Daraktan rukunan kamfanonin Dangote Devakumar Edwin ya tabbatar da cewa sun fara sayar da man dizel da man jiragen sama a ƙasar. Edwin ya shaida wa Reuters cewa "Muna da isasshen mai. Ana jigilar man ta ruwa da ƙasa. Jiragen ruwa na bin layi ɗaya bayan ɗaya don ɗiban dizel da man jiragen sama." "Jiragen ruwa na ɗaukar lita miliyan 26, amma muna ƙoƙarin ganin an kawo jiragen da ke ɗaukar lita miliyan 37 don sauƙaƙa ayyukan." Ƙungiyar masu sayar da man ta amince kan sayar da kowacce litar dizel naira 1,225 bayan ƙulla yarjejeniya kan tsayar da farashi, in ji Abubakar Maigandi, Shugaban ƙungiyar Masu Sayar da Man Fetur Mai Zaman Kanta a Nijeriya. Mambobin ƙungiyar na da gidajen mai kimanin 150,000 a faɗin Nijeriya, in ji Maigandi. Matatar mai ta Dangote na so ta kawo ƙarshen dogaro ga man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje da Nijeriya ke yi. Nijeriya ce kasar da ta kowace yawan jama'a a Afirka, kuma tana kan gaba a tsakanin ƙasashen da ke fitar da albarkatun mai, amma tana sayo mai daga waje saboda ba ta da matatu.