الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Matatar Dangote ta fitar da man fetur a karon farko zuwa Kamaru

Kamfanin makamashi na Kamaru Neptune Oil ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa inda ya ce kamfanonin biyu na nazari domin samar da tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen daidaita farashin man fetur da samar da damammaki a fadin yankin. Kamfanin mai na Dangote ya sanar da cewa a karon farko ya f...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:17 ص
Matatar Dangote ta fitar da man fetur a karon farko zuwa Kamaru
لمحة سريعة

Kamfanin makamashi na Kamaru Neptune Oil ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa inda ya ce kamfanonin biyu na nazari domin samar da tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen daidaita farashin man fetur da samar da damammaki a fadin yankin. Kamfanin mai na Dangote ya sanar da cewa a karon farko ya f...

Kamfanin makamashi na Kamaru Neptune Oil ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa inda ya ce kamfanonin biyu na nazari domin samar da tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen daidaita farashin man fetur da samar da damammaki a fadin yankin. Kamfanin mai na Dangote ya sanar da cewa a karon farko ya fitar da man fetur zuwa Kamaru, wanda hakan ake sa ran zai buɗe wata hanya da za ta taimaka wurin samun wadataccen man fetur da kuma daidaita farashi a yankin. Sai dai kamfanin na Dangote bai bayar da cikakken bayani ganga nawa aka fitar ba. Kamfanin samar da makamashi na kasar Kamaru Neptune Oil a cikin wata sanarwar da ya fitar ya bayyana cewa, dukkanin kamfanonin biyu suna nazari domin samar da tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen daidaita farashin man fetur da samar da damammaki a fadin yankin. Neptune Oil ya ce an aiwatar da cinikin samar da mai ba tare da masu shiga tsakani ba. Matatar man ta Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kullum na da burin yin gogayya da matatun mai na Turai idan ta soma aiki gadan-gadan.