Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Matar Shugaban Kasar Turkiyya ta yi bikin murnar Ranar Mata ta Duniya

Mata suna shuka iri a cikin kasa kuma suna da kyakkyawan fata ga al’umma, suna nuna tasirinsu a kowane fanni, su ne ginshikin zaman lafiya mai dorewa da adalci a duniya, in ji Emine Erdogan. Matar Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan ta mika sakon murnar zagayowar Ranar Mata ta Duniya, wato biki...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:17
Matar Shugaban Kasar Turkiyya ta yi bikin murnar Ranar Mata ta Duniya
En bref

Mata suna shuka iri a cikin kasa kuma suna da kyakkyawan fata ga al’umma, suna nuna tasirinsu a kowane fanni, su ne ginshikin zaman lafiya mai dorewa da adalci a duniya, in ji Emine Erdogan. Matar Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan ta mika sakon murnar zagayowar Ranar Mata ta Duniya, wato biki...

Mata suna shuka iri a cikin kasa kuma suna da kyakkyawan fata ga al’umma, suna nuna tasirinsu a kowane fanni, su ne ginshikin zaman lafiya mai dorewa da adalci a duniya, in ji Emine Erdogan. Matar Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan ta mika sakon murnar zagayowar Ranar Mata ta Duniya, wato bikin da ake yi duk shekara dangane da nasarorin da mata suke samu. “A wannan rana ta Mata ta Duniya ina farin cikin taya mata masu tsayuwar daka da ke kawo sauyi da ci gaba murna,” kamar yadda Emine Erdogan ta bayyana a shafinta na X a ranar Juma’a. Ta ce mata suna shuka iri a cikin kasa kuma suna da kyakkyawan fata ga al’umma, suna nuna tasirinsu a kowane fanni, “su ne ginshikin zaman lafiya mai dorewa da adalci a duniya.” “Duk wata nasara tana samuwa ne saboda jajircewarsu, muna da kwarin gwiwar hango makomarmu,” in ji Emine Erdogan. Kowace ranar 8 ga watan Maris, ana murnar zagayowar bikin martaba nasarorin da mata suka samu da kuma wayar da kan jama’a kan daina nuna musu wariya.